Lissafi ya nuna cewa Najeriya na fita daga matsin tattalin arziki – Ministan Kudi

Lissafi ya nuna cewa Najeriya na fita daga matsin tattalin arziki – Ministan Kudi

A jiya Juma’a, 2 ga watan Yuni ministan kudin Najeriya, Kemi Adeosun, tace lissafi na nuna cewa Najeriya na fita daga cikin matsin tattalin arzikin.

Mrs. Adeosun tayi wannan bayani ne a kan tashar talabijin na Channels.

Tace: “ Ina ganin muna fit daga matsin, dukkan lissafi sun nuna hakan amma abin da yafi muhimmanci shine muna kan turban kawo cigaba Najeriya da zai taimaki rayuwar gobe.”

Mrs. Adeosun ta bayyana cewa shugaba Buhari ya gaji matsaloli da yawa lokacin da ya hau mulki wadanda ke zama cikas ga cimma manufa cigaban kasa.

Lissafi ya nuna cewa Najeriya na fita daga matsin tattalin arziki – Ministan Kudi

Lissafi ya nuna cewa Najeriya na fita daga matsin tattalin arziki – Ministan Kudi

“Mun gaji matsaloli da dama,ai tattali arzikin Najeriya ba karamin gyara take bukata ba amma aikin tiyata na kwarai kuma za’a kwan biyu kafin ta warke.”

KU KARANTA: Janar Bamaiyi ya tona asirin Farfesa Yemi Osinbajo

Ministan ya kara da cewa dalilin da ya sa kayan masarufi sukayi tashin gwauron zabo shine tsadar kudin mota wajen tafiyar da kayan gona zuwa birane.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel