Rikici tsakanin Musulami da Kirista ya sabbaba kulle jami’ar Katsina

Rikici tsakanin Musulami da Kirista ya sabbaba kulle jami’ar Katsina

Wata rikicin addini tsakanin mabiya addinin Kirista da mabiya addinin Islama ya sabbab kulle jami’ar gwamnatin tarayya da ke Dutsinma jihar Katsina.

Rikicin tayi kamari ne a jiya Juma’a bayan an idar da salla wasu daliban jami’an suka fara zanga-zanga kan mabiya addinin kiristan da ke aiki a jami’an.

Andrew Moses, wani jami’in tsaron makarantar ya bayyanawa manema labarai cewa, “ Muga wasu sabbin fuskoki inda ma’aikatan jami’ar ke zaune har da shugaban makarantan. Da muka tambayesu abinda ya kawo su, sai sukace, ‘ Mun zo jihadi ne akan kiristocin jami’ar nan.”

Mr. Moses yace da wuri ya sanar da shugabansu sai aka sanar da hukumar yan sandan. Wani malami a jami’ar wanda aka sakaye sunansa ya bayyana cewa ai da dadewa akwai rikici a jami’ar sanadiyar tuhumar da akeyiwa tsohon shugaban makarantan, James Ayatse, na daukan mabiya addininsa da yawa aiki a jami’ar.

Rikici tsakanin Musulami da Kirista ya sabbaba kulle jami’ar Katsina

Rikici tsakanin Musulami da Kirista ya sabbaba kulle jami’ar Katsina

Malamin ya kara da cewa rikicin yau ta taso ne yayinda kotu ta mayar da tsohon shugaban makarantan, Haruna Kaita bayan an tsigeshi sanadiyar almundahana.

KU KARANTA: Tashin hankali, sata a coci

Wata majiya ta bayyana cewa Kaita ya shigo jami’ar da mutane domin yakan kiristocin makarantan.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel