Biafra: Ba zaku iya raba Najeriya ba yanzu – Shehu Sani ga IPOB, MASSOB

Biafra: Ba zaku iya raba Najeriya ba yanzu – Shehu Sani ga IPOB, MASSOB

Sanata mai wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawan tarayya, Shehu Sani , ya bayyana ra’ayinsa cewa Najeriya ba zata iya rabuwa yanzu ba.

Dan majalisan yayi wannan magana ne a taron kwalejin ilimi FCE, Zaria, Kaduna.

Ya baiwa yan kungiyar IPOB shawara suyi hakuri da wannan batu na rabewa.

Yace : “ Matasa su dauna darasi daga wadanda suka samu nasara a rayuwa ba wadanda suka fadi ba. a wasu yanayin, babu abinda mutm zai dauke face darasi.

Biafra: Ba zaku iya raba Najeriya ba yanzu – Shehu Sani ga IPOB, MASSOB

Biafra: Ba zaku iya raba Najeriya ba yanzu – Shehu Sani ga IPOB, MASSOB

“Ana bukatan abubuwa da yawa daga Najeriya, ba zaku iya raba wannan kasa yanzu ba.”

Sanatan yayi kira ga gudanar da shirye-shiryen wayar da kai wanda zai ilmantar da matasa akan watsi da rashawa wanda ya zama cikas ga cigaban tattalin arzikin kasa.

KU KARANTA: Yardua yayi wata babban kuskure a gwamnatinsa - Osinbajo

Yace : “Ana bukatan garambawul da hanulan mutane. Yaki da rashawa bai zai isar ba ta hanyar kama mutane da gurfanar da su amma ta hanyar canza tunanin yan Najeriya.

“Wajibi ne mu canza halin son duniyanmu, muna bukatan al’umma da ke gine kan girmama juna, soyyayan kasa, da kuma hadin kai.”

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel