Kungiyar kwallon kafa ta Najeriya tayi kasa-kasa da kasar Togo da ci 3 da nema

Kungiyar kwallon kafa ta Najeriya tayi kasa-kasa da kasar Togo da ci 3 da nema

- Kungiyar kwallon kafa ta kasa super Eagle ta samu nasarar akan abokiyar karawarta ta kasar Togo da ci 3:0 da nema a wani wasan sada zumunci da suka buga a birnin Paris.

- A karon farko mai horar da yan wasan Najeriya Gernot Rohr, ya buga wasa ba tare da manyan yan kwallon kungiyar ta Super Eagle ba kamar su,John Mikel Obi, Ogenyi Onazi,Victor Moses da kuma mai tsaron gida Carl Ikeme.

Wasan na jiya na daga cikin wasannin da mai horarwa Gernot Rohr ya shirya domin gwajin yan wasan, kafin wasan cancantar shiga kofin nahiyar Afirika na shekarar 2019 da kungiyar zata buga a karshen mako mai zuwa da kasar Afirika ta kudu a garin Uyo dake jihar.

Kungiyar kwallon kafa ta Najeriya tayi kasa-kasa da kasar Togo da ci 3 da nema

Kungiyar kwallon kafa ta Najeriya tayi kasa-kasa da kasar Togo da ci 3 da nema

NAIJ.com ta samu labarin cewa dan wasa Ahmed Musa, da ya angwance makon da yagabata ya samu nasarar jefa kwallo biyu,a minti na uku da fara wasan da kuma minti na ashirin da uku.

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester City, Kelechi Iheanacho, shine ya samu nasarar jefa kwallo ta uku.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel