Gwamnatin tarayya ta yi gargadin bullar cutar murar tsuntsaye a Jihohi 7

Gwamnatin tarayya ta yi gargadin bullar cutar murar tsuntsaye a Jihohi 7

- Gwamnatin tarayya ta ce dole a dakatar da shigo da kaji domin guje ma yaduwar cutar

- Har ila yau gwamnatin tarayya ta ce zuba matakan tsaro da sauran su zai taimaka gurin rage yaduwar annobar

Bayan bullowar cutar murar tsuntsaye, gwamnatin tarayya, ta sanar da ‘yan Najeriya jihohin da ke fama da bullar cutar.

A lokacin da ya gana da kwamishinonin harkan noma na jiha a babban birnin tarayya Abuja a ranar Juma’a, 2 ga watan Yuni, Mshelbwala ya ce dole a dakatar da shigo da kaji domin guje ma ci gaba da damuwar cutar.

Jihohin da Mshelbwala ya lissafa sun hada da Bauchi, Kano, Katsina, Nasarawa, Filato. Kaduna da kuma Birnin Tarayya, Abuja. Ya ce a ranar 30 Ga Mayu din nan ne jihar Kaduna ta kawo rahoton bullar cutar a jihar.

Gwamnatin tarayya ta yi gargadin bullar cutar murar tsuntsaye a Jihohi 7

Gwamnatin tarayya ta yi gargadin bullar cutar murar tsuntsaye a Jihohi 7

Ya ce wannan cutar murar tsuntsaye, ta game jihohi 26 da Abuja, ta fara bulla ne tun cikin shekarar 2008, inda ya shafi gonakin kiwon kaji har 800 a cikin kananan hukumomi 123 a fadin kasar nan.

Ya ce har yanzu ba a kai ga samun wani magani na rigakafin wannan murar tsuntsaye ba. Ya da ice za a gaggauta killace wadanda ba su kamu ba, kuma ya ja kunnen cewa akwai sakacin masu kiwon kaji ta hanyar kin yin amfani da wasu dabarun kiwon kaji.

Daraktan ya ce gwamnatin tarayya ta biya kudin diyya ga wadanda kajinsu suka yi fakat har naira milyan 674 ga manomi 269 a inda annobar ta yi illa.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli bidiyon NAIJ.com da ke lissafo nasarorin shugaba Buhari a shekaru biyu

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel