Babbar magana! An kama wasu mutane 3 bisa zargin yin sata a coci

Babbar magana! An kama wasu mutane 3 bisa zargin yin sata a coci

- An kai karan wasu mutane 3 zuwa babban kotun yankin Gudu da ke babban birnin tarayya Abuja akan laifin sata wani coci.

- Mutanin 3, Hamza Salihu, Akorede Babalola da Isaac Aboyomi an caje su da laifuka gudu 2 wanda suka hada da laifin hadin kai da kuma sata.

Mista Fidelis Ogbode, mai gabatar da karar, ya gaya ma kotu cewa Mr. Austin Abua, babban jami’in tsaro na cocin mai suna Our Lady Queen of Nigeria Pro-Cathedral Church wanda ke Garki a babban birnin tarayya Abuja ya kai rahoton lamarin ga ofishin ‘yan sanda na Garki a 27 ga watan Mayu 2017.

NAIJ.com ta samu labarin cewa ya ce daya daga cikin wadanda ake zargi, Hamza Salihu, a lokacin da yake cikin cocin, ya saka hannun cikin jakar daya daga cikin masu bauta a wurin ya dauke mata wayar ta da kudi naira N25,000.

Babbar magana! An kama wasu mutane 3 bisa zargin yin sata a coci

Babbar magana! An kama wasu mutane 3 bisa zargin yin sata a coci

A cewar mai gabatar da karar, an kama Hamza a lokacin da yake aikata laifin bayan an ma shi tambayoyi ya tona asirin sauran ‘yan uwan na shi.

Ogbobe ya ce laifin ya saba wa sashe 343 da kuma 287 daga cikin dokokin Final.

Duk da haka, kowanne daga cikin masu laifin su 3 sun ce basu aikata laifukan da ake tuhumarsa da su ba

Mai hukunci, Mr Umar Kagarko, ya bada beli kowanne daga cikin wadanda ake zargi (wadanda ke kare kansu) akan kudi naira N100,000.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel