Shinkafa mai guba ta mamaye Najeriya – Kungiyar Gwamnonin Najeriya

Shinkafa mai guba ta mamaye Najeriya – Kungiyar Gwamnonin Najeriya

- Kungiyar gwamnonin Nijeriya (NGF) ta koka akan yadda gurbatacciyar shinkafa mai guba ta mamaye kasuwannin Nijeriya, inda ta bukaci hukumar hana fasakaurin kayayyaki da ta dauki matakin gaggawa game da al’amarin.

- Gwamonin sun koka akan yadda gubar da ke shinkafar ka iya kisa ko ta haifar da rashin lafiya, ga wadanda suka yi amfai da ita.

A wata sanarwa da mai kula da harkokin yada labarai na kungiyar Abdulrazak Bello-Barkindo ya fitar, ya ce kungiyar ta tattauna akan wannan batu ne a ganawar da ta yi ta karshe a Abuja.

Kungiyar ta ce wasu daga cikin samfurin shinkafar da ke shigowa kasar a yanzu tun lokacin mulkin Goodluck a 2014 aka saye su, a lokacin, gwamnati ta karfafawa masu sayo shinkafa da yawa daga kasashen waje gwiwa.

NAIJ.com ta samu labarin cewa a ganaawar ta su ta karshe, gwamnonin sun gayyaci kwamftrola janar na kwastan, Kanal Hameed Ali da ya zo ya yi masu karin haske game da yadda hukumar ke yunkurin dakile shigowar shinkafar.

Shinkafa mai guba ta mamaye Najeriya – Kungiyar Gwamnonin Najeriya

Shinkafa mai guba ta mamaye Najeriya – Kungiyar Gwamnonin Najeriya

Kwamftrollan, wanda mataimakinsa Dangaladima Aminu ya wakilta ya jaddada wa kungiyar gwamnonin cewa suna iya kokarin su, duba da yadda mutanen da ke zaune a garuruwan da ke kan iyakoki suke taimakawa masu fasakaurin.

Gwamnonin sun ce tuni wasu jahohi suka yi nisa a yunkurin su na ciyar da kan su, wanda hakan zai iya rage yadda ake sayen gurbatattun shinkafar na kasar waje.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyauta

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyauta

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel