YANZU YANZU: Allah ya yi ma mahaifiyar Obanikoro Wasilat rasuwa

YANZU YANZU: Allah ya yi ma mahaifiyar Obanikoro Wasilat rasuwa

Allah ya yi ma Alhaja Wasilat Obanikoro, mahaifiyar wani tsohon ministan tsaro na jiha, Sanata Musiliu Obanikoro, rasuwa.

NAIJ.com ta tattaro cewa Alhajan wacce aka fi kira da Iya Lati ta rasu a safiyar yau Asabar, 3 ga watan Yuni bayan ta yi fama da dan takaitaccen rashin lafiya, ta rasu tana da shekaru 95.

Ta kasance mai siye da siyarwa a baya sannan kuma tana zaune a gidanta dake Isale-Eko inda a nan ne ta rasu.

Za’ayi jana’izarta a yau da karfe 3 na rana a makabartan Ikoyi a Lagas daidai da koyarwan addinin Islama.

KU KARANTA KUMA: Lai Muhammed yayi bayanin dalilan da yasa gwamnatinsu ke kin bin umarnin kotuna

Iya Lati ta rasu ta bar ‘ya’ya , jikoki d tattaba kunne da dama.

A rahoton baya, Obanikoro, wanda ya yi aiki a matsayin minista a karkashin gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya ce zai bar jam’’iyyar PDP idan kotu ta tabbatar da Ali Modu-Sheriff a matsayin shugaban jam’iyyar.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli wannan bidiyo na NAIJ.com kan rikicin Ile-Ife

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel