Lai Muhammed yayi bayanin dalilan da yasa gwamnatinsu ke kin bin umarnin kotuna

Lai Muhammed yayi bayanin dalilan da yasa gwamnatinsu ke kin bin umarnin kotuna

- Lai Muhammed yayi bayanin dalilan da yasa gwamnatinsu ke kin bin umarnin kotuna, yace sai an dubi harkokin tsaron kasa kafin azo na hakkokin bil-adama

A zaman taunawa da yake da wata kafar jarida a Abuja, Ministan yada al'adu da labarai na kasa, Alh. Lai Mohammed, yace a matsayinsa na lauya, ya san dole ya girmama kotu, kuma ya fahimci karfinta, amma yasan ba komai suka gama sani ba a batun wadanda ake tuhuma, don haka hukuncinsu gurdadde ne.

"Dole ne mu dubi hakkin zaman lafiyar al'umma kafin mu dubi hakkokin kammammen mutum daya, su masu bada hukuncin basu da faffadar masaniya game da illar wadanda muke zarga", inji shi.

Yana dai bayani ne kan batun kin sako tsohon mai baiwa shugaba Goodluck Jonathan shawara kan harkokin tsaro, Kanal Sambo Dasuki, da kuma shugaban kungiyar musulman shi'a masu biyayya ga kasar Iran, Malam Ibrahim El-Zazzaki na Zariya, wadanda aka kama su shekaru biyu da suka gabata aka kuma ki sako su duk da umarnin kotu na ayi hakan.

KU KARANTA KUMA: Atiku ya zama sabon Wazirin Adamawa, yayinda da dansa ya zamo Turaki

Lai Muhammed yayi bayanin dalilan da yasa gwamnatinsu ke kin bin umarnin kotuna

Lai Muhammed yayi bayanin dalilan da yasa gwamnatinsu ke kin bin umarnin kotuna

Ana dai zargin gwamnatin Buhari da kin girmama doka da biris da take hakkokin dan-adam, zaarin da ministan ya musanta.

"Ya zaka zarge mu da mulkin kama karya? bayan nima Lauya ne, na kuma san aikin kotu, na kuma san ilolin wadannan talikai? gwamnati ta fi kotuna sanin bayanan sirri a kan wadannan mutane, don haka ake ajje dasu har yanzu", ya kara da cewa.

Ana dai tuhumar Sambo Dasuki da wawaso da kasa kudin kasa ga mukarraban gwamnati, da ma handama. Shi kuma El-Zazzaki ana tuhumarsa da ta'addanci da cin amanar kasa.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel