'Yan bindiga sun sace hakimi a Kaduna, tare da iyalansa

'Yan bindiga sun sace hakimi a Kaduna, tare da iyalansa

- Hare-hare da garkuwa da jama'a ta zama ruwan dare a Najeriya

- An sace hakimi a kudancin Kaduna, kuma dansa yace wasu fulani ne sukayi aika-aikar

- An harbe mai tsaron hakimin har lahira yayin harin

Rahotanni dake fitowa daga Kukau dake karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna, na cewa an zo har gida an sake hakimin yankin tare da iyalinsa da yaransa an tsere dasun sai dai har yanzu ba'a san ko su waye ba, kuma basu turo sakon ko me suke so ba.

Da ga Hakimin Nathan Makama, mai shekaru 35, ya bayyana cewa, a ranar juma'a aka sace mahaifinsa da mahaifiyarsa da yaransu, kuma yace yaren hausa yaji suna yi da karin fillanci.

Ya kuma kara da cewa, dakaren da yayi kokarin kare mahaifin nasa ya rasa ransa a arangamar.

'Yan bindiga sun sace hakimi a Kaduna, tare da iyalansa

'Yan bindiga sun sace hakimi a Kaduna, tare da iyalansa

Da aka tuntubi hukumar yan sanda ta yankin dai sunce basu sami rahoto ba kab batun tukunna, amma zasu bayar da bayani da zarar sunyi bincike.

KU KARANTA KUMA: Yadda wani mai yankan kumba yayi lalata da dan almajiri a jihar Bauchi

A yankuna da yawa na jihar Kaduna dai, ana yawan samun matsalolin tsaro, da tashin-tashina tsakanin al'ummu dake zaune a jihar, kabilanci, addinanci da siyasa yana iya zama sanadiyyar yaki da barnar dukiyoyi tsakanin kabilu, shekara da shekaru.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli wannan bidiyo da NAIJ.com ta kawo maku:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel