Mutan Najeriya na cikin kuncin talauci, amma sun yarda da Buhari - Shehu Sani

Mutan Najeriya na cikin kuncin talauci, amma sun yarda da Buhari - Shehu Sani

- Sanata Shehu Sani dan rajin kare Dimokuradiyya ne, da kare hakkin dan Adam

- Ana sa ran Sanatan zai nemi takarar Gwamnan Kaduna a nan gaba

- Shehu Sani da Gwamna El-Rufa'i sun raba gari tun bayan zaben 2015

A siyasar kaduna dai bata chanza zani ba, tun bayan tafiyar shugaba Buhari jinya kasar waje, jiga-jigai biyu na jam'iyyar APC mai mulkin jihar na nan suna sa kafar wando daya, da kuma nuna wa talakawa wa yafi kusa da shugaba Buhari, tsakanin Sanata Shehu Sani da Malam Nasiru.

An dai jiyo Shehu Sani na cewa lallai mulkin nan ya jefa talakkawa a cikin talauci, ya kuma kuntata wa jama'a, amma duk da haka, talakkawa basu gaji da salon mulkin shugaba Buhari ba.

KU KARANTA KUMA: Lai Muhammed yayi bayanin dalilan da yasa gwamnatinsu ke kin bin umarnin kotuna

'Mutan Najeriya na cikin kuncin talauci, amma sun yarda da Buhari'

'Mutan Najeriya na cikin kuncin talauci, amma sun yarda da Buhari'

Wannan ba shine karo na farko ba, dama chan an saba jin kushe ko suka daga Malam Shehu Sani, dama Malam Nasiru Gwamna ga shugaba Buhari kan batun talauci da talakawa ke ciki.

Amma a wannan karon, shugaba Buhari ya sami yabo, inda Sanatan mai wakiltar Kaduna ta tsakiya ke cewa koda dai talakawa na ganin tasku, sun yarda dari bisa dari da Buhari, kuma suna tare dashi, kuma ko gobe shine zabinsu.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

NAIJ.com ta kawo maku bidiyo kan yadda kayan marmari suka yi tashin gwauron zabi a kasuwa sakamakon azumin Ramadan

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel