Hukumar yan sandan jihar Bauchi tayi ram da gungun makasa 4

Hukumar yan sandan jihar Bauchi tayi ram da gungun makasa 4

Ofishin hukumar yan sanda jihar Bauchi ta damke wasu yan taki zama 4 masu kashe jama’a. kwamishana yan sandan jihar, Garba Umar ne ya bayyana hakan yayinda yake bayani ga manema labarai a hedkwatan yansanda da ke Bauchi.

Umar yace an damke su ne gungun bisa ga wata labarin leken asirin da suka samu.

Yace : “A ganawar masu ruwa da tsaki na karshen baya da nayi da kungiyar Miyetti Allah a jihar, nayi kira da su cewa su bayyana wadanda suka hallaka masu garkuwa da mutanen da ake damke da uma masu satan shanu a jihar amma sukace musanta saninsu.

“Mutanen sun kasance suna yanke hukunci da akansu, zasu je kauyuka a ayarinsu kuma su kama mutane su kashe su akan abubuwan da basu taka kara suka karya ba.

Hukumar yan sandan jihar Bauchi tayi ram da gungun makasa 4

Hukumar yan sandan jihar Bauchi tayi ram da gungun makasa 4

“Da wannan abu ya fara yawa, sai hukuma ta shi runduna ta musamman domin dakile su. A ranan 26/5/2017 misalin karfe 6 na safiya, an damke wasu a tsaunin Runde a Bauchi.

KU KARANTA: An birne dan sandan Najeriya a raye a Legas

“Sunayen wanda aka kama shine, Adamu Abubakar, (52) (shugabansu), Muhammad Lawan, (52), Ahmadu Gambo, (38) and Mohammed Tukur, (50), dukkansu yan Galambi."

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyauta

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyauta

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel