Kalli matashiya dake tsananin bukatar taimako domin a ceto rayuwar ta (HOTUNA)

Kalli matashiya dake tsananin bukatar taimako domin a ceto rayuwar ta (HOTUNA)

Matashiya Maryam Abubakar na bukatar taimako domin a ceci rayuwar ta. Ta kasance ma'aikaciya ce a asibitin kwararru dake jihar Sokoto.

Maryam na fama da ciwon kansar koda inda take jinya a kasar Indiya sama da shekara guda. Tun daga lokacin da take jinya 'yan uwanta ne suke jinyarta. Inda a duk wata ake kashe kimanin naira dubu dari tara na kudin jinyarta, wanda kuma kowa ya san hakan ba abu ne mai sauki ba.

Iyayenta da 'yan uwanta sun karar da dukiyarsu wajen jinyarta har ta kai ga sun sayar da kadarorin da suka mallaka duk don su ceci rayuwar Maryam. Kuma yanzu haka kusan makonni uku kenan babu kudin da za a biya kudin maganin.

Kalli matashiya dake tsananin bukatar taimako domin a ceto rayuwar ta (HOTUNA)

Kalli matashiya dake tsananin bukatar taimako domin a ceto rayuwar ta

Maryam dai tana bukatar a yi mata tiyata don ganin an cire mata koda, wanda akalla kudin aikin cire kodar ya kai kimanin naira milyan hudu (N= 4,000,000:00).

Kalli matashiya dake tsananin bukatar taimako domin a ceto rayuwar ta (HOTUNA)

Kalli matashiya dake tsananin bukatar taimako domin a ceto rayuwar ta)

Don haka muke kira ga gwamnatin jihar Sokoto karkashin jagorancin Aminu Waziri Tambuwal, Sanatocin jihar, 'yan majalisun jihar da sauran masu hannu da shuni na jihar da su taimaka su ceci rayuwar wannan matashiya.

Kalli matashiya dake tsananin bukatar taimako domin a ceto rayuwar ta (HOTUNA)

Maryam Abubakar na tsananin bukatar taimako domin a ceto rayuwar ta

Sannan kuma bincike ya nuna cewa takardar bukatar tallafawa Maryam ya isa ga gwamnan Tambuwal amma har yanzu bai samu damar sanya hannu a takardar ba don ganin an fitar da kudin aikin.

Baya ga haka kuma al'umma kuma ba a bar ku a baya ba, ga duk mai halin taimakawa Maryam kofa a bude take, kama daga taro ko sisi.

Ga masu bukatar taimakawa Maryam ga akawun din da za a tallafa mata

Naira Account details:

Account name: Maryam Abubakar

Account number: 0027059466 (Savings acct/GTBANK)

Dollar Account details:

Account name: Maryam Abubakar

Account number: 0239673298 (Current/GTBANK)

Don karin bayani za a iya tuntubar lambar wayar 'yar uwar Maryam wato Farida; 0803189 8240

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel