Ramadan: Ribadu da Magu zasu tattauna muhimmancin yaƙi da rashawa a watan

Ramadan: Ribadu da Magu zasu tattauna muhimmancin yaƙi da rashawa a watan

- Kungiyar yan jaridu Musulmai, MMPN ta shirya taron bita akan yaki da rashawa

- Pantami, Magu, Ribadu da minista zasu halarci taron

Kungiyar yan jaridu Musulmai, MMPN ta shirya taron bita, karo na na goma sha biyu kamar yadda ta saba yi a duk shekara cikin watan Ramadan, inji rahoton Premium Times.

Shugaban kungiyar Abdur-Rahman Balogun ne ya sanar da hakan inda yace taron bitan zai gudana ne a ranar Asabar 3 ga watan Yuni.

KU KARANTA: Zuwa da kai ba saƙo ba: Ɗan Najeriya yaje birnin Landan don yin dubiya ga Buhari

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito shugaban kungiyar yana bayyana taken bitan wannan shekarar da suna ‘Yaki da rashawa: wane rawa yan jaridu zasu taka?’

Ramadan: Ribadu da Magu zasu tattauna muhimmancin yaƙi da rashawa a watan

Ribadu da Magu

Balogun yace bitan na shekarar nan zata karkata ne kan hanyoyin yaki da rashawa, da kuma yadda za’a samar da ingantattun tsare tsare na magance matsalar rashawa a kasar nan.

Taron na bana zai gudana ne a dakin taro na babban Masallacin kasa dake Abuja, kuma zai samu halartan manyan baki kamar su shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu, tsohon shugaban EFCC, Nuhu Ribadu a matsayin shugaban Taro, da shugaban hukumar kimiyyar sadarwa ta Najeriya, Sheikh Ibrahim Pantami.

Hakazalika ana sa ran halartan mashawarcin shugaban kasa kan yaki da rashawa Farfesa Sagay, shugaban hukumar JAMB, Ishaq Oloyede, Malam Nurudeen Abdul-Malik, tsohon shugaban Muryar Najeriya Malam Abubakar Jijiwa da kuma ministan Abuja Muhammad Bello.

Shugaban kungiyar yace ana tsammanin halartan kungiyoyin Musulunci da kamfanunuwan jaridu da dama, sa’annan ya kara dacewa manufar sanya batun rashawa a matsayin darasin bita a bana ne sakamakon barazanar da matsalar ke yi ma Najeriya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Zaka iya auren kabila?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel