Jinyar Buhari na tayar da kura a Najeriya, inji jaridar Wall Street Journal

Jinyar Buhari na tayar da kura a Najeriya, inji jaridar Wall Street Journal

- Jaridar Wall Street Journal ta waiwayi Najeriya

- Shugaba Buhari na jinya a asibiti, kusan dukka shekararnan

- Batun bangaranci da addinanci da kabilanci ya sake dawowa fagen siyasar Najeriya

A duk lokacin da aka fara fuskantar zabe, a Najeriya, sai an sami batun kabilanci da na bangaranci, kai harma da na addinanci, domin ko da ba'a fada da baka ba, Najeriya kasa ce dake rabbare akan wannan shati.

Wakiliyar Jaridar kasar Amurka ta Wall Street Journal mai ofishi a birnin New York, dake Abuja, babban birnin Najeriya, Alexandra Wexler, tayi sharshi akan lafiyar Buhari da ma dambarwar siyasar da ke tafe a zaben 2019, inda ta waiwayi abubuwan da aka saba gani a baya a Najeriya, dama hanga abin da ka iya zuwa a nan gaba.

A rahoton nata, Miss Wexlerta ce, Kasa mafi girman tattalin arziki a fadin Nahiyar Afirka ta sake fadawa halin rashin tabbas a siyasa, tun bayan barin shugaba Buhari kasar domin jinya a kasar Ingila a farkon watan Mayu.

KU KARANTA KUMA: Lai Muhammed yayi bayanin dalilan da yasa gwamnatinsu ke kin bin umarnin kotuna

Jinyar Buhari na tayar da kura a Najeriya, inji jaridar Wall Street Journal

Jinyar Buhari na tayar da kura a Najeriya, inji jaridar Wall Street Journal

A cewarta: "Dan hobbasar da mataimakinsa wanda kuma daga addinin Kirista ta fito, ya kara zama tunzuri ga masu mara wa shugaba Buharin baya, wanda shi musulmi ne. An kuma fara ganin alamun rarrabuwar ra'ayoyi tun ma daga can kololuwar dattijan siyasar kasar."

A dai fadin Ms. Wexler: "Koda yake ba a rubuce yake ba, amma mulki na zagawa ne tsakanin al'ummu biyu na Musulmi da na Kirista, kuma ana zagawa dashi ne bangarori daban daban na kasarnan don a sami maslaha da yarda da juna tsakanin kabilun kasar."

A bincikenta, ta gano makamanciyar dambarwar da ta faru shekaru kusan goma da suka shude lokacin da maras lafiya Umaru Yar'aduwa ya hau mulki, kuma ya gagara mulkin saboda jinya, wanda daga karshe dai ya rasu akan wa'adinsa na farko, wanda hakan ya kara tunzura musulmi na kasar, har ta kai ga sake zabo musulmi dan arewa kafin hankula su kwanta a arewacin kasar.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli wannan bidiyo na NAIJ.com kan nasarori da shugaba Muhammadu Buhari ya samu a shekaru biyu da ya yi yana mulki a kasar:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel