Ba zan hakura da kira ga mutane da nake yi da su canza halayyarsu ba – Sarkin Kano

Ba zan hakura da kira ga mutane da nake yi da su canza halayyarsu ba – Sarkin Kano

- Sarkin Kano Muhammadu Sanusi ya ce ba zai gaza ba gurin kira ga mutane da su canza halayyarsu

- Ya bayyana cewa da wuya mutane su yarda da wani sabon abu musamman idan sun saba da yadda suke a ko ina ne a fadin duniya

- Sarki Sanusi ya kalubalanci iyaye da su mai da hankali wajen tarbiyantar da ‘ya’yansu domin rashin hakan kan kawo matsalolin fyade da akeyi wa yara kanana

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi ya ce ba zai gaza ba gurin kira ga mutane da su canza halayyarsu. Ya fadi hakan ne a yayinda yake zantawa da sabon shugaban Asusun tallafawa yara na majalisar dinkin duniya UNICEF,a fadar sa dake garin Kano.

NAIJ.com ta samu labarin cewa Sarkin Sanusi ya ce da wuya mutane su yarda da wani sabon abu musamman idan sun saba da yadda suke a ko ina ne a fadin duniya.

A cewar sa: “A sani cewa akwai mutane da yawa da suka fahimci inda na sa a gaba kuma suna goya mun baya dari bisa dari. Domin haka ina kira ga kungiyoyi, Dalibai, ma’aikatu da malaman addini da su goya mini baya akan irin canji da nake so in kawo ga Al’umma.

Ba zan hakura da kira ga mutane da nake yi da su canza halayyarsu ba – Sarkin Kano

Sarkin Kano ya ce ba zai hakura da kira ga mutane da nake yi da su canza halayyarsu ba

“Sannan kuma na san zan samu nasara akan haka domin abune mai inganci nake yi wa al’ummar."

KU KARANTA KUMA: Ka da ka so ka ji yadda Jakadan Kasar Birtaniya ya yabi ‘Yan Najeriya

Baya ga haka kuma Sarkin ya kalubalanci iyaye da su mai da hankali wajen tarbiyantar da ‘ya’yansu domin rashin hakan kan kawo matsalolin fyade da akeyi wa yara kanana da dai sauransu.

Shugaban ‘UNICEF’ na kasa, Mohammed Fall ya yi godiya ga sarki Sanusi kan irin karramawar da yayi musu kuma ya ce UNICEF za ta ba Sarki duk irin gudumnawar da yake bukata domin samun nasara akan aikin da ya sa a gaba.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel