'Kiris ya rage su yanka ni' - Dan Majalisar Kano da aka sace

'Kiris ya rage su yanka ni' - Dan Majalisar Kano da aka sace

- Bai fadi nawa aka biya don fansarsa ba, amma ance sun bukaci N60m

- Barayin su kai 14 kuma dauke da muggan makamai

- Sun sace shi ne a Jere, hanyarsa ta zuwa Kano

Tun bayan sako shi da masu garkuwa da shi da suka yi, Garba Umar Durbunde, dan Majalisar Kano mai wakiltar Sumaila/Takai a majalisar Tarayya, yace sai da ya kwana a asibiti domin razana da yayi, bayan shafe kwana daya a hannun muggan.

An dai sace shi ne a hanyarsa ta zuwa Kano daga Abuja, a Jere, garin kaduna, barayin kuma sun kai su 14 a fadin sa, yace kuma bayan kama shi da suka yi, sun yi daji dashi tsahon tafiyar awoyi hudu cikin dare.

KU KARANTA KUMA: Ba zan hakura da kira ga mutane da nake yi da su canza halayyarsu ba – Sarkin Kano

'Kiris ya rage su yanka ni' Dan Majalisar Kano da aka sace

'Kiris ya rage su yanka ni' Dan Majalisar Kano da aka sace

"Sun ce in ban biya miliyan sittin ba zasu yanka ni, bayan da suka gane ni da hulla ta ja ta Kwankwasiyya, suka ce ni dan siyasa ne na Kwankwaso" ya fadi wa majiyar NAIJ.com.

Duk da dai bai fadi ko nawa aka caje shi ba kafin fansarsa, wasu majoyoyi na cewa an hada miliyan 10.

"Wannan mugun abu bana fatansa ga kowa domin banyi bacci ba tun lokacin da abun ya faru, sai da naje asibiti", ya fadi ma 'yan jarida.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel