Kotu ta wanke Okah daga laifin cin amanar kasa

Kotu ta wanke Okah daga laifin cin amanar kasa

- Kotu ta wanke Charles Okah wanda ake zargi da kitsa harin bam da aka kai ranar 1 ga watan oktoban 2010 a birnin Abuja

- Ana kuma zargin Charles Okah da Obi Nwabueze da hannu a wani harin da aka kai ranar 15 ga watan maris na 2010 a garin Warri

- Lauyoyin da ke kare Charles Okah sun bayyana gamsuwarsu da matakin da kotu ta dauka

Lauyoyin da ke kare Charles Okah wanda ake zargi da kitsa harin bam da aka kai ranar 1 ga watan oktoban 2010 a birnin Abuja, sun bayyana gamsuwarsu da matakin da kotu ta dauka na yin watsi da daya daga cikin zarge-zargen da ake yi masa saboda rashin gabatar da hujjojin da ke tabbatar da wanda ake zargi na da hannu a lamarin.

Lauyan Okah Alex Izinyon, wanda ke magana da manema labarai jim kadan bayan da kotu ta sanar da yin watsi da karar, ya ce laifufuka biyu da ake zargin wanda yake karewa, wato cin amanar kasa da kuma ta’addanci, amma sun yi nasara a kan daya daga cikinsu, kuma sauran zance ya rage a hannun mai shigar da kara na gwamnati.

KU KARANTA: An bankado wata wabbar badakala ta N423biliyan a gwamnatin ‘Yar'adua da Jonathan

Kotu ta wanke Okah daga laifin cin amanar kasa

Charles Okah wanda ake zargi da kitsa harin bam da aka kai ranar 1 ga watan oktoban 2010 a birnin Abuja

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, Charles Okah da kuma wani mai suna Obi Nwabueze, ana zarginsu da hannu a wani harin da aka kai ranar 15 ga watan maris na 2010 a garin Warri na jihar Delta, inda ake tuhumarsu da yunkurin kashe tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan da kuma wasu gwamnoni da ke taro a jihar ta Delta.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Bayan shekaru 50; shin masu fafutukan ganin sun kafa kasar Biyafara daga Najeriya za su ci nasara kuwa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel