Zuwa da kai ba saƙo ba: Ɗan Najeriya yaje birnin Landan don yin dubiya ga Buhari

Zuwa da kai ba saƙo ba: Ɗan Najeriya yaje birnin Landan don yin dubiya ga Buhari

- Wani masoyin shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi tattaki har birnin Landan

- Mutumin yaje ne domin yayi ma shugaba Buhari fatan alheri

Wani babban masoyin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Cif Sunbo Onitri yayi tattaki takanas-ta-Kano har zuwa masaukin shugaban kasa ‘Abuja House ‘ dake dake Birnin Landon don mika masa takarda.

Kamar yadda Rabiu Biyora ya kawo rahoton, masoyin na shugaba Buhari ya je ne don ya mika ma shugaba Buhari wasikar ‘Allah ya kara sauki, inda a cikin takardar yayi wa shugaba Buhari fatan samun sauki da wuri da kuma dawowa gida Nijeriya don cigaba da tafiyar da mulki.

KU KARANTA: Abin mamaki: Yarinya mai shekaru 12 ta haihu jaririya a bola

Wani hadimin shugaban kasa ne aka aiko ya fito ya karbi wasikar tare da mika ta ga shugaba Buhari a ranar 29 ga Mayu, 2017.

Zuwa da kai ba saƙo ba: Ɗan Najeriya yaje birnin Landan don yin dubiya ga Buhari

Mutumin a kofar masaukin Buhari

Ko a satukan da suka gabata NAIJ.com ta kawo muku rahoton da wani bature ya kai ma shugaban kasa kwatankwacin wannan ziyara, inda ya kai masa furanni, wanda hakan alama ne na yi masa fatan Alheri.

Ga sauran hotunan:

Zuwa da kai ba saƙo ba: Ɗan Najeriya yaje birnin Landan don yin dubiya ga Buhari

Yana jira

Zuwa da kai ba saƙo ba: Ɗan Najeriya yaje birnin Landan don yin dubiya ga Buhari

Mutumin dauke da wasikar

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Zaku iya auren bare?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel