Takaran gwamna 2019: ‘Idan ba Shehu Sani ba, bama yi’ – Matasan Kaduna

Takaran gwamna 2019: ‘Idan ba Shehu Sani ba, bama yi’ – Matasan Kaduna

- Matasan jihar Kaduna sun bukaci Shehu Sani daya fito musu takarar gwamnan jihar Kaduna

- Sun bayyana haka ne yayin wata ziyarar mubaya’a da suka kai masa a gidansa dake Kaduna

Daruruwan matasan jihar Kaduna daga yankin Zaria ne suka bukaci sanatan Kaduna ta tsakiya Sanata Shehu Sani daya fito musu takarar gwamnan jihar Kaduna a shekarar 2019.

Matasan sun bayyana haka ne yayin wata ziyarar mubaya’a da suka kai masa a gidansa dake Kaduna a ranar Laraba 31 ga watan Mayu, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA: Wani babban Fasto ya tunjuma cikin kogi da niyyar kashe kansa

Matasan sun bayyana tsananin tausayin talaka dayake ji da kuma farin jinin al’umm dayake dasu a matsayin abubuwan da suka sanya shi zama zakaran gwajin dafi.

Takaran gwamna 2019: ‘Idan ba Shehu Sani ba, bama yi’ – Matasan Kaduna

Shehu Sani

Shugaban matasan, Alhaji Yakubu Umar yace bukatar da suke da shi na ganin an inganta jihar Kaduna tare da ciyar da ita gaba ne ya sanya su jaddada goyon bayansu ga sanata Shehu Sani.

“Da mutane kwara bakwai kacal muka fara wannan tafiyar, amma yanzu yayan kungiyar sun daruruwa, don a yanzu haka mun watsu daga Zaria zuwa Soba, Sabongari, Ikara, Giwa, Saminaka da sauran garuruwa.” Inji shi.

Dayake nasa jawabin, majiyar NAIJ.com ta ruwaito mai gayya mai aiki, Sanata Sani yana gode ma matasan da suka kawo masa ziyara, kuma yace zai duba bukatarsu idan lokaci yayi, sa’annan ya caccaki lamirin gwamnatin jihar na siyar da gidajen gwamnati.

“Ya zama wajibi a garemu mu saurari wadanda suka zabe mu, kuma mu tattauna nasarorin da muka samu da kuma kalubalen dake gaban mu.” Inji Sanata.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

An bankado dangantakar Sanata Dino Melaye da wata yarinya

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel