To fa! An kama dan sanda da jami'in soja dumu-dumu da laifin fashi da makami

To fa! An kama dan sanda da jami'in soja dumu-dumu da laifin fashi da makami

- Rundunar ‘yan sandan jahar Oyo ta cafke wani Insfekta da jami’in rundunar sojan Nijeriya Herbert Mbachumai shekaru 55, da kofur Sikiru Balogun mai shekaru 46 da laifin fashi da makami.

- Haka kuma an kama sauran tawagar ‘yan fashin, wadanda suka shahara wajen tare tankokin man fetur a kan manyan titinan jahar gari Ibadan da ke jahar Oyo.

Yayin da yake magana da manema labarai, kwamishinan ‘yan sandan jahar Abiodun Odude ya ce sun samu Naira miliyan 1.2 a wajen ‘yan fashin, tare da motoci biyu kirar Honda da wayar Nokia guda daya.

To fa! An kama dan sanda da jami'in soja dumu-dumu da laifin fashi da makami

To fa! An kama dan sanda da jami'in soja dumu-dumu da laifin fashi da makami

NAIJ.com ta samu labarin cewa ya ce daga shekarar 2016 zuwa yanzu, ‘yan fashin sun kwace akalla tankokin mai guda 6 makil daman fetur da za a yi safarar zuwa sassan kasar nan.

Ya ce jami’an tsaron da ke cikin su korarru ne, amma sun ci gaba da amfani da kakin soja da dan sanda wajen yaudarar mutane su yi masu fashi.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel