Yan majalisar dattawa sun bukaci a kara kudin man fetur zuwa N150

Yan majalisar dattawa sun bukaci a kara kudin man fetur zuwa N150

- Sanatocin Najeriya yan kwamitin kula da ayyuka sun bayar da shawarar a kara kudin man fetur a kasar nan daga N145 zuwa N150.

- Sanatocin sun ce hakan ne kawai zai sa a samu kudin da za'a iya ida ayyukan more rayuwa da gwamnati ta sa a gaba kamar hanyoyi.

Sanatocin sunce karin kudin na N5 sune za'a rika ajiyewa a wani asusu ko gidauniya ta musamman da zata rika kula dahanyoyin kasar nan.

NAIJ.com ta samu labarin cewa dai wannan shawarar ta karin kudin na mai ya fito be daga shugaban kwamitin ayyuka na majalisar Sanata Kabiyu Gaya daga Kano.

A jiya ne dai aka so a tattauna akan batun amma kuma sai aka tsallake batun saboda kurewar lokaci.

Yan majalisar dattawa sun bukaci a kara kudin man fetur zuwa N150

Yan majalisar dattawa sun bukaci a kara kudin man fetur zuwa N150

Senatocin da suka amince da wannan shawarar kuma suka rattaba hannu a rahoton kwamitin sun hada da Kabiru Gaya, Clifford Ordia, Barnabas Gemade, Mao Ohuabunwa , Bukar Abba Ibrahim, Ben Bruce, Gilbert Nnaji, Abubakar Kyari, Ibrahim Danbaba, Mustapha Bukar, Sani Mustapha da kuma Buruji Kashamu.

Sauran Sanatocin dake a kwamitin amma kuma basu saka hannu akan rahoton ba sune Olusola Adeyeye, Biodun Olujimi da kuma Ahmad Ogembe.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel