2019: Sule Lamido muke fata, inji wani dan siyasa na yankin Neja Delta

2019: Sule Lamido muke fata, inji wani dan siyasa na yankin Neja Delta

- Wani dan siyasa a yankin Niger Delta, Afoke Akporua ya bayyana tsohon gwamnan jahar Jigawa, Alhaji Sule Lamido a matsayin wanda suke fatan cewa zai lashe kujerar shugaban kasa a zaben 2019.

- Akporua wanda ya na daya daga cikin ‘yan kungiyar yakin neman zabe na jam’iyyar PDP a zaben 2015, ya jaddada cewa mutanen yankin Niger Delta ba su da wani dan takara da ya wuce Sule Lamido.

NAIJ.com ta samu labarin cewa a wata hira da ya yi da manema labarai jim kadan bayan ya gana da jiga jigan ‘yan Niger Delta mazauna jahar Lagos, Okporua ya ce Jagoran talakawan (Lamido) sananne ne a kowanne lungu da sako na yankin Niger Delta.

Ya ce lokaci ya kurewa duk wani mai niyyar yin takarar shugaban kasar domin kuwa ba zai iya samun karbuwa a yankin ba, kamar yadda Lamido ya samu karbuwa.

2019: Sule Lamido muke fata, inji wani dan siyasa na yankin Neja Delta

2019: Sule Lamido muke fata, inji wani dan siyasa na yankin Neja Delta

Ya ci gaba da cewa mutane yankin sun zabi Lamido ne saboda babu wani dan takara da ke son su fiye da shi. Ya ce Lamido ya kan ziyarci yankin a kai kai domin ya kara wa gwamnoni su karfin gwiwa ya kuma tabbatar da an zauna lafiya.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel