Jihar Yobe tayi asarar biliyan 15 kan yaki da Boko Haram

Jihar Yobe tayi asarar biliyan 15 kan yaki da Boko Haram

- A yaki da Boko Haram, an sami asarar dukiyoyi sosai a yankunan da abin ya shafa

- Yobe na daga cikin jihohin da basu da arziki a Najeriya

- Boko Haram ta ja baya da hare-hare a Yola

Gwamnan jihar Yobe Ibrahim Geidam ya ce jiharsa ta kashe kusan Naira biliyan goma shabiyar a kan yaki da ta'addanci a cikin shekaru 3 da suka wuce, yace mafi yawan kudin an kashe su ne a kan aikin gyare gyare na barnar da haren-hare suka yi wa jama'a.

Ya fadi hakan ne a lokacin da yake karbar tawagar 'yan majalisar wakilai ta tarayya a fadar gwamnati, wadanda suka zo duba yadda gyare gyare ke tafiya tun bayan korar mayakan daga jihar.

KU KARANTA KUMA: Ka da ka so ka ji yadda Jakadan Kasar Birtaniya ya yabi ‘Yan Najeriya

Jihar Yobe tayi asarar biliyan 15 kan yaki da Boko Haram

Jihar Yobe tayi asarar biliyan 15 kan yaki da Boko Haram

Tawagar ta duba wuraren da abun ya shafa, da kuma matsugunnai na 'yan gudun hijira, sun kuma yaba wa gwamnan kan ci gaba da suka gani a kasa.

A wani al'amari na daban, NAIJ.com ta rahoto cewa Allah ya tona asirin wani boka daya kware wajen baiwa yan fashi sa’a mai suna Abdulrazak Buhari dake Sabon Gida jihar Katsina, inda shi kansa sa’arsa ta kare, ya shiga hannun jami’an Yansanda.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito wannan boka shike yi ma yan fashin dake tare hanyar Funtua zuwa Zaria aiki, kuma boka Buhari ya bayyana ma jaridar cewar N30,000 yake amsa daga hannun barayin a duk aikin da yayi musu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Shin kuna ganin za'a cimma yankin Biyafara?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel