Dalilin da ya sa Buhari ya zabi a kula da shi a asibitin Landan – Lai Mohammed

Dalilin da ya sa Buhari ya zabi a kula da shi a asibitin Landan – Lai Mohammed

- Ministan bayanai da al’adu, Lai Mohammed ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari na bukatar kulawar likita mafi inganci

- Ministan ya ba ‘yan Najeriya tabbacin cewa shugaban kasa Buhari na hannun kwararru a birnin Landan

Ministan bayanai da al’adu, Lai Mohammed, ya yi bayani kan dalilin da ya sa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fi son tafiya birnin Landan don samun kulawa da lafiyarsa, yayinda ya yi burus da asibitocin Najeriya.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Lai Mohammed ya ba da bayanin a lokacin wani shiri na gidan radiyo mai taken , ‘Morning Crossfire’, a tashar Nigeria Info Abuja 95.1FM, a ranar Alhamis, 1 ga watan Yuni.

A lokacin shirin wani fusataccen mutun ya soki gwamnatin APC da ta saba ma alkawarinta da hana jami’an gwamnati tafiya kasar waje domin duba lafiyarsu.

Dalilin da ya sa Buhari ya zabi a kula da shi a asibitin Landan – Lai Mohammed

Lai Mohammed ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari na bukatar kulawa mafi inganci ta fannin lafiya

A yayinda ya ke maida martani, Mohammed ya ce shugaban kasar ya tafi neman magani a kasar waje ne saboda ya na bukatar kulawa na musamman.

KU KARANTA KUMA: Ka da ka so ka ji yadda Jakadan Kasar Birtaniya ya yabi ‘Yan Najeriya

“Amsa na mai sauki ne sosai. Shugaban kasar mahaifinmu ne, shine jagoran kasar sannan kuma a gani na ya cancanci kulawar mafi inganci ta fannin lafiya."

A halin da ake ciki, gwamnatin tarayya ta ba yan Najeriya tabbacin cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari na hannun kwararru a birnin Landan.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

NAIJ.com ta kawo maku biyo na nasarorin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu a shekaru biyu da ya yi yana mulki:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel