Ba mamaki Gwamnati ta saki Kanal Dasuki da Zakzaky

Ba mamaki Gwamnati ta saki Kanal Dasuki da Zakzaky

– Ba a dade da Kotu ta bada belin Nnamdi Kanu Jagoran Biyafara ba

– Sai dai har yanzu Sambo Dasuki da El-Zakzaky su na nan a garkame

– Muna tunani Watakila su ma a sake su kwanan nan

Kuna sane cewa har yau dai Gwamnati ta ki sakin Sambo Dasuki

Haka kuma Shugaban Kungiyar IMN ta Shi’a na garkame

Farfesa Sagay ya nemi a kyale su idan kotu ta bada umarni

Ba mamaki Gwamnati ta saki Kanal Dasuki da Zakzaky

Shugaban Kungiyar IMN Zakzaky

Farfesa Itse Sagay wanda yana cikin masu ba shugaban kasa shawara a kan harkokin yaki da sata yayi kira da Gwamnati ta saki su Sambo Dasuki da Ibrahim El-Zakzaky. Sagay din kamar yadda ku ka sani ya goyi bayan abin da Kungiyar Lauyoyi su ka fada.

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari muguwa ce Inji Dino Melaye

Ba mamaki Gwamnati ta saki Kanal Dasuki da Zakzaky

Gwamnati ta ki sakin Kanal Dasuki har yanzu

Itse Sagay ne shugaban masu Shugaba Buhari shawara game da irin wadannan harkoki ya kuma nemi Gwamnati ta sake su ko ta daukaka kara tun da kotu ta bada belin su. Ba mamaki a tunanin mu dai Gwamnatin ta ji shawarar sa don kuwa da alamu Shugaban kasar na jin maganar sa.

Wani tsohon Gwamna a lokacin mulkin Soji Kanal Dangiwa Umar mai ritaya ya taba cewa zai yi wahala a saki Dasuki ko ayi masa adalci a kotu. Gwamnati dai ta fake ne da sha’anin tsaro wajen cigaba da rufe wadannan mutane.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Shekaru 50 da Yakin Biyafara; Obasanjo da Osinbajo sun yi magana

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel