Tattalin arziki: Kudin kasar wajen Najeriya ya kara yin kasa

Tattalin arziki: Kudin kasar wajen Najeriya ya kara yin kasa

– Asusun kudin kasar wajen Najeriya na kara rage yawa

– Yanzu haka Dala biliyan 30.49 ya rage

– Babban bankin kasar ya bayyana haka

A yanzu haka Najeriya na da Dala Biliyan 30.49 a asusun kudin waje

Kudin kasar wajen Najeriya dai na kara ja baya

A watan jiya Najeriya na da Dala Biliyan 30.52

Tattalin arziki: Kudin kasar wajen Najeriya ya kara yin kasa

Kudin kasar wajen Najeriya na ja baya bayan ya tashi

Babban bankin kasar na CBN yace kudin kasar wajen Najeriya ya dan kara sauka kasa daga Dala Biliyan 30.52 zuwa Dala biliyan 30.49. Hakan ya nuna cewa kudin kasar ya ja baya da kasa da kashi 1%.

KU KARANTA: Osinbajo ya kai ziyara Garin Kuros-Riba

Kudin kasar wajen dai bai taba sauka kasa haka ba cikin kusan watanni biyu da su ka wuce. Tattalin arzikin Najeriya na ta faman tangal-tangal kawo yanzu. Babban bankin na CBN na amfani da abin da aka samu wajen kokarin rage farashin Dala a kasuwa.

Hakan kuma dai zai sa darajar Naira ta kara sauka kasa kamar yadda kwanaki ta koma N382 wanda da a baya tana kan N380. Girgizar asusun kasar wajen ne dai ya sa darajar Naira ke kara fadi kasa a kasuwar canji.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ko Dala ta taba zama daya da Naira kuwa?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Surukar marigayi Bilyaminu, Maimuna Aliyu tana kotu bisa tuhumar wawurar dukiyar gwamnati

Surukar marigayi Bilyaminu, Maimuna Aliyu tana kotu bisa tuhumar wawurar dukiyar gwamnati

Surukar marigayi Bilyaminu, Maimuna Aliyu tana kotu bisa tuhumar wawurar dukiyar gwamnati
NAIJ.com
Mailfire view pixel