Kasafin kudin 2017: Yadda Ministocin Buhari su ka hana Osinbajo sa hannu

Kasafin kudin 2017: Yadda Ministocin Buhari su ka hana Osinbajo sa hannu

– Ashe Ministoci ne su ka hana Farfesa Osinbajo ya sa hannun kan kasafin bana

– Da alamu an yi wasu kare-kare ne a cikin kasafin

– Don haka ne Ministoci su ka nemi a dakata tukun

Jiya mu ka ji Fadar Shugaban kasa tace ba a gama aiki game da kasafin kudi ba

An dai sa rai jiya za a rattaba hannu kan kundin kasafin na wannan shekara

Sai dai yanzu mun fara jin cewa an samu sauyi ne daga abin da su ka bada

Kasafin kudin 2017: Yadda Ministocin Buhari su ka hana Osinbajo sa hannu

Kasafin kudi: Majalisa ta rage abin da Ministoci su ka ware

Mun ji labari cewa ba mamaki an dan buga wani aringizo ne ko an yi wata ‘yar badakala a cikin kasafin kudi. Don haka ne ma Ministocin kasar su ka nemi cewa ka da Mukaddashin Shugaban kasa ya sa hannun sa tukun. Ministoci sun ga cewa Majalisa ta rage kudin da su ka ware.

KU KARANTA: Majalisa ta laftawa 'Yan Najeriya haraji

Kasafin kudin 2017: Yadda Ministocin Buhari su ka hana Osinbajo sa hannu

Kasafin kudi: Har yanzu ba a gama aiki ba – Inji Osinbajo

Tun kwanaki dama mun ji kishin-kishin din cewa wa wasu ‘Yan Majalisa sun cusa abubuwa da Shugaban kasa bai sa ba. Ba dai yau aka fara samun badakala a harkar kasafin kudin kasar ba. Ko a bara haka aka dauki dogon lokaci ana ta fama.

Dama jiya ne Farfesa Yemi Osinbajo yace har yanzu yana cigaba da tuntubar ‘Yan Majalisu game da kasafin kudin. Mai magana da bakin Farfesan watau Laolu Akande ya tabbatar da cewa har yanzu dai ba a kammala aikin kasafin kudin ba.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Abubuwan da Gwamnatin Buhari tayi cikin shekaru 2 [Bidiyo]

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Surukar marigayi Bilyaminu, Maimuna Aliyu tana kotu bisa tuhumar wawurar dukiyar gwamnati

Surukar marigayi Bilyaminu, Maimuna Aliyu tana kotu bisa tuhumar wawurar dukiyar gwamnati

Surukar marigayi Bilyaminu, Maimuna Aliyu tana kotu bisa tuhumar wawurar dukiyar gwamnati
NAIJ.com
Mailfire view pixel