Wannan gwamnatin mugaye ce - Inji Dino Melaye

Wannan gwamnatin mugaye ce - Inji Dino Melaye

- Dino Melaye dan adawar cikin gida ne a APC

- Ya zabi gidan Sanata saraki a maimakon gidansu Bola Tinubu

- Yace gwamnatin Buhari makare take da muggai

An jiwo dan Majalisa Sanata Dino Melaye yana caccakar gwamnatin Buhari, inda ya kira ta da gwamnatin dake cike da masu aikata laifuka.

Yace "Ai a baya mun fuskanci gwamnatin 'yan handama ne a mulkin shugaba Jonathan, amma a wannan lokacin muna zaune ne a gwamnatin gaggan masu laifi, in ka duba yadda za'a sami sakataren gwamnati da handamar makudan kudade, da sunan yanke ciyawa."

KU KARANTA KUMA: Samari na kokarin zama baki a kasarsu - Inji tsohon Gwamna Donald Duke

Wannan gwamnatin mugaye ce, inji Dino Melaye

Wannan gwamnatin mugaye ce, inji Dino Melaye

Ya kuma kira rahoton Sahara Reporters na jin wata murya na maganar baiwa joji cin hanci kan batun tuhumarsa da ake, da cewa ba muryanrsa bace, kuma kage ce.

An dai sami rarrabuwar kai a cikin gida na APC tun bayan da suka ci zabe aka zo batun shugabanci a cikin majalisa, su Melaye suka hada kai da jam'iyyar PDP suka kafa nasu juyin mulkin na cikin gida.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel