Wani babban Fasto ya tunjuma cikin kogi da niyyar kashe kansa

Wani babban Fasto ya tunjuma cikin kogi da niyyar kashe kansa

- Faston garin Bafia dake kasar Kamaru, Jean Marie Benoit Balla ya hallaka kansa

- Faston ya hallaka kansa ne ta hanyar tunjumawa cikin wata katafariyar raf

Wani babban Faston garin Bafia dake kasar Kamaru, Jean Marie Benoit Balla ya hallaka kansa ta hanyar tunjumawa cikin wata katafariyar rafi mai sun Rafin Sanaga daga kan gadar Ebebda.

Mabiya cocin Faston ne suka bazama suna neman Limamin nasu bayan sun tsince motarsa ajiye a kan gadar Ebebda a ranar Laraba 31 ga watan Mayu, kimanin kilomita 900 daga Yaounde, babban birnin kasar.

KU KARANTA: Gwamnati ta samar da dokoki guda 9 da zasu taƙaita zuƙan sigari (KARANTA)

Jaridar Daily Trust ta ruwaito sakamakon binciken da aka gudanar a cikin motar an gano takardun shaidan dan kasa, takardun motar sa da sauran muhimman takardu a motar.

Wani babban Fasto ya tunjuma cikin kogi da niyyar kashe kansa

Faston da motarsa

Amma daga bisani an tsinci wata takarda a cikin motar inda Faston ya rubuta cewar shifa ya fada cikin ruwa, kamar yadda majiyar NAIJ.com ta ruwaito.

Wani babban Fasto ya tunjuma cikin kogi da niyyar kashe kansa

Jama'a na jimami a gefen motarsa

Nan da nan bayan watsuwar rahoton sai gwamnan yankin Naseri Paul Bea da sauran shuwagabannin gwamnati suka isa wajen da lamarin ya faru tare da jami’an tsaro.

Shima DPO Yansanda yace ya samu rahoton ne daga wajen wani babban Fasto, wanda ya sanar da shi bacewar abokin nasu da misalin karfe 1 na rana.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

An tona dangantakar dake tsakanin Dino Melaye da wata budurwa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel