Gwamnati ta samar da dokoki guda 9 da zasu taƙaita zuƙan sigari (KARANTA)

Gwamnati ta samar da dokoki guda 9 da zasu taƙaita zuƙan sigari (KARANTA)

- Gwamnati ta koka kan yawaitan mashaya sigari a Najeriya

- Za’a fara ƙaddamar da dokoki guda 9 da zasu hana shan sigari a Najeriya

Ministan kula da kiwon lafiya, Isaac Adewole ya sanar da wasu dokoki guda tara wadanda gwamnati zata fara kaddamarwa domin rage ta’ammali da sigari a Najeriya, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Ministan ya bayyana dokokin guda tara da suna ‘National Tobacco Act’ wanda yace tsohon shugaban kasa Jonathan ne ya rattafa hannu akan dokokin tun a shekarar 2015, amma ba’a kaddamar ba.

KU KARANTA: Ba’a gayyaci Mikel da Moses ba a fafatwar da Najeriya zata yi da Afirka ta Kudu

Ministan ya bayyana ma majiyar NAIJ.com an samu tsaiko wajen kaddamar da dokoin sakamakon wasu karin tsare tsare da ake bukatar majalisa ta sanya hannu akai. Ga dai dokokin nan, guda 9:

Gwamnati ta samar da dokoki guda 9 da zasu taƙaita zuƙan sigari (KARANTA)

Sigari

1- Hana siya da siyarwar Sigari ga duk wanda bai kai shekaru 18 ba

2- hana siyar da Sigari guda daya, sai dai guda 20

3- Ba za’a siyar da Sigari mara hayaki ba har sai ya kai gram 30

4- Hana cinikayyar siya da siyawar Sigari a shafukan yanar gizo

5- Dakatar da kamfanunuwan Sigari daga shiga harkar Lafiya

6- Hana busa Sigari a bainar Jama’a, ko duk inda jama’a ke taruwa kamar su makaranta, Asibiti, wajen wasan yara, wajen shakatawa, manyan shaguna, filin wasanni, dakunan cin abinci da sauransu.

7- Kamawa da gurfanar da duk mutumin daya mallaki ireiren wuraren da aka ambata, kuma ya bari aka sha Sigari a cikinsu.

8- Hana tallar Sigari da kawayenta

9- Tabbatar da an bi tsare tsaren da suka dace wajen hada Sigarin

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Zaka iya auren dan wata kabila daban?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel