Ta’amuni da muggan kwayoyi ya fara yawa cikin ‘yan mata

Ta’amuni da muggan kwayoyi ya fara yawa cikin ‘yan mata

Matsalar shaye-shaye tsakanin matasa, musamman mata, ta zama ruwan dare a arewacin Najeriya bisa ga gurbacewan tarbiyya.

Bayan fuskantar kalubalen rashin son yi karatu da yan mata keyi, ta’amuni da muggan kwayoyi da shaye-shaye ya zama babban ciwon kai ga iyaye a arewacin Najeriya.

Wakilinmu a Adamawa Ibrahim Abdul’aziz, ya shirya ma na wannan rahoton:

Wakilin muryar Amurka da ke Adamawa Ibrahim Abdul’aziz, ya shirya ma na wannan rahoton:

“Kamar yadda alkalumman hukumar yaki da sha da fataucin muggan kwayoyi, wato NDLEA ke nunawa, matasa masu jini a jika su suka fi fadawa wannan mummunan dabi’a ta shan kwaya.

Baya ga matsalar yan jagaliya, yanzu wata matsalar da ke addabar jama’a ita ce ta shaye-shayen miyagun kwayoyi musamman tsakanin ‘yan matan da ka iya zama iyaye nan gaba.

koda yake hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi, NDLEA, ta sha shirya taruka da gangamin yaki da wannan mugunyar dabi’a, da alamar har yanzu da sauran rina a kaba, kamar yadda ‘yan mayen suka tabbatar.

Masana dai na danganta wannan dabi’ar ne da rashin kulawar iyaye da kuma tarayya da abokanan da basu dace ba.

Ta’amuni da muggan kwayoyi ya fara yawa cikin ‘yan mata

Ta’amuni da muggan kwayoyi ya fara yawa cikin ‘yan mata

Alhaji Abdullahi Hassan Zungeru tsohon jami’in hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ne wato NDLEA, wanda ya rike jihohi da dama kafin yayi murabus. Ya ce tun da aka soma siyasa kananan yara suka shiga shaye-shayen miyagun kwayoyi, ciki harda yan mata, batun da ya ce ba zai haifar da da mai ido ba.

KU KARANTA: Solomon Dalung ya halarci tafsiri a Abuja

To wai ko wace illa shan kwayan ke da ita, musamman ga mata? Malama Salmah Tahir wata malamar jinya a Yola, ta ce:

Baya ga birkita kwakwalwa, kwayar na da wasu munanan illoli. Su kuwa sarakuna iyayen al’umma na fa nuna damuwarsu ce ganin cewa lamarin na kara kazanta. Alh. Muhammad Inuwa Baba Paris, Hakimin Jimeta kuma Dan Isan Adamawa ya ce yanzu haka wadannan matasa na neman zama alakakai ga kansu da kuma al’umma baki daya.’’

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Surukar marigayi Bilyaminu, Maimuna Aliyu tana kotu bisa tuhumar wawurar dukiyar gwamnati

Surukar marigayi Bilyaminu, Maimuna Aliyu tana kotu bisa tuhumar wawurar dukiyar gwamnati

Surukar marigayi Bilyaminu, Maimuna Aliyu tana kotu bisa tuhumar wawurar dukiyar gwamnati
NAIJ.com
Mailfire view pixel