Samari na kokarin zama baki a kasarsu - Inji tsohon Gwamna Donald Duke

Samari na kokarin zama baki a kasarsu - Inji tsohon Gwamna Donald Duke

- Samari su fito a dama dasu a sabon zubi, inji Donald Duke

- Donald Duke na son zama shugaban kasa

- Donald Duke ya ce gwamnatoci sun rena samari

A taron da aka gudanar a jihar Legas a satin da ya gabata, an jiyo tsohon gwaman Donald Duke na shinshinar sake takarar shugabancin kasar nan, ya kuma ce tafiyar dole da samari za'ayi, ya yi kira da samari suzo a dama dasu, domin a cewar sa gwamnatoci sun rena samari.

Ya kara da cewa: "Samari su dena barin ana ware su a harkar mulki, kuma su dena zama kamar suna zaman haya a kasarsu, su fito a dama dasu".

KU KARANTA KUMA: Mulkin Buhari ne ya sa ni fataucin 'hodar iblis' - wani Inyamuri

Samari na kokarin zama baki a kasarsu, inji tsohon Gwamna Donald Duke

Samari na kokarin zama baki a kasarsu, inji tsohon Gwamna Donald Duke

NAIJ.com ta tuna cewa, a shekarun 2006/2007 Donald Duke ya nemi takarar shugabancin kasa amma aka dauko tsohon shugaba Goodluck Ebele aka bashi mataimakin shugaban kasa. daga wancan lokacin dai Donald Duke yayi tsit a fagen siyasa.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Nasarorin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu a shekaru biyu da ya yi kan mulki

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyauta

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyauta

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel