'Yan Najeriya sun fara gajiya da Buhari'

'Yan Najeriya sun fara gajiya da Buhari'

- Reno Omokri ya rena shugaba Buhari

- Reno tsohon dan adawa ne na jam'iyyar PDP, ga APC

- Sannan kuma yana zama a kasar Amurka

A lokacin da mulkin jam'iyyar APC yazo karshen wa'adinsa, inda za'a fara fuskantar zabuka na cikin gida cikin watanni shida, a 2018, masu adawa da salon mulkin shugaba Buhari na kara karaji a fagen siyasar kasar nan.

A wata sanarwa da ya fitar, Reno Omokri, wanda tsohon mai taimakawa tsohon shugaba Jonathan ne, yace an gaji da mulkin APC, mutane sun gaji da shugaba Buhari, ya fadi hakan ne a shafinsa na sadarwa na facebook.

KU KARANTA KUMA: Mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya isa Calabar

'Yan Najeriya sun fara gajiya da Buhari'

'Yan Najeriya sun fara gajiya da Buhari'

"Ko a fagen jin ra'ayoyin jama'a, da jam'iyya mai mulki ta fitar, ya nuna cewa 51 cikin dari na wadanda aka ji ra'ayoyinsu, sunce basu gamsu da salon mulkin Buhari ba' wanda ke nuna a cewarsa, 'mutan Najeriya sun gaji da shugaban nasu.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Nasarorin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu a shekaru biyu da ya yi kan mulki

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel