Sojoji sun bindige wani dan kunar bakin wake a Maiduguri

Sojoji sun bindige wani dan kunar bakin wake a Maiduguri

- Wani dan kunar bakin wake ya yi kokarin tada bam a kusa da barikin soji na Giwa Barracks dake Maiduguri.

- Shugaban kungiyar ‘yan banga wato ‘Civilian-JTF’, Danbatta Bello ya fada wa majiyar mu cewa a ranar Talata da misalin karfe 2:40 na rana sojoji sun harbe wani dan kunar bakin waken a lokacin da ya ke kokarin shiga cikin bariki domin ya tada bam din.

“Mun kai gawan dan kunan bakin waken dakin ajiyan gawawwaki na wani asibiti a Maiduguri.”

Sojoji sun bindige wani dan kunar bakin wake a Maiduguri

Sojoji sun bindige wani dan kunar bakin wake a Maiduguri

NAIJ.com ta samu labarin cewa Danbatta Bello ya ce hakan ya faru ne a daidai lokacin da wasu mazaunan sansanin Konduga ke jana’izan wasu ‘yan uwansu biyar da Boko Haram ta yi wa yankan rago a ranar Litini.

Ya ce an gane cewa mutanen da Boko Haram ta yi wa yankan ragon mazaunan kauyen Balle Shuwari ne dake karamar hukumar Konduga.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel