Matsalar Ta'addancin fulani makiyaya na iya zama sabuwar Boko Haram - Inji Sanata

Matsalar Ta'addancin fulani makiyaya na iya zama sabuwar Boko Haram - Inji Sanata

- Yawancin Mahara fulani suna kai hari a kan kauyuka ne da dare, su kone kome su kashe kowa

- Ana samun karuwar hare-hare lokacin da ake fara aikin gona, a daminar bana

- Ana kokarin magance lamarin da kare iyakoki

A kokarin gwamnati na kawo karshen yaki da ta'addanci, an yi kira ga gwamnati da ta bada fifiko kan yaki da harin fulani makiyaya.

Kiran yazo ne daga bakin Sanata Clifford Odia, daga Edo central a lokacin zaman majalisar, wanda ya goya wa batun baya shine Sanata Francis Elimikhena, Edo North.

KU KARANTA KUMA: Idan ka ji abin da ‘Yan Najeriya su ka yi asara a tsarin MMM sai ka yi kuka

Matsalar Ta'addancin fulani makiyaya na iya zama sabuwar Boko Haram, inji Sanata

Matsalar Ta'addancin fulani makiyaya na iya zama sabuwar Boko Haram, inji Sanata

NAIJ.com ta tattaro inda ya ke cewa wadannan fulani suna kisa, sata, fyade da barnar dukiya: "Wannan wani sabon kalubale ne irin na Boko Haram, kuma idan ba'a tari abun da wuri ba, zai iya zamowa babbar matsala kamar dai ta Boko Haram."

Ya kuma bayyana cewa, akwai hanyoyin ma da ba'a iya bi a yanzu a jihar Edo, akwai kuma gonaki da an dena noma su saboda ta'addancin masu hare-haren, yace wannan dole ya kau.

Ya kara da cewa dole Insipekta Janar na yan sanda ya bawa lamarin sabuwar nutsuwa domi a kaucewa tabarbarewar lamarin tun wuri.

Su dai makiyaya na zargin ana sace musu shanu ne ko kuma ana kashe musu yara masu kiwo.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel