Sojojin Turkiyya 13 sun salwanta a hatsarin jirgin sama

Sojojin Turkiyya 13 sun salwanta a hatsarin jirgin sama

- Jirgin saman sojin kasar Turkiyya ya gamu da mummunar hadari

- Jirgin yayi hadarin ne bayan yaci karo da wayar wuta jim kada da tashin sa

Kimanin Sojoji 13 ne suka riga mu gidan gaskiya daga kasar Turkiyya, inda jirgin su yaci karo da wata wayar lantarki jim kadan da tashinsa wani kaye dake kudancin kasar.

Jaridar Gulf News ta ruwaito jirgin sama mai tashin angulu, kirar AS532 Cougar ya fadi ne a kan iyakar kasar Iraq, inda ya kashe dukkanin Sojojin dake cikinsa, kamar yadda hukumar Sojin kasar ta sanar.

KU KARANTA: Takara 2019: Matasan jihar Kano sun yi kira da babban murya ga Kawu Sumaila

“Gwarazan Sojojin mu sun yi shahada a wani hatsarin jirgin sama mai tashin Angulu” Inji Rundunar Sojin kasar.

Sojojin Turkiyya 13 sun salwanta a hatsarin jirgin sama

Hatsarin jirgin sama

Sai dai majiyar NAIJ.com ta bayyana cewar bincike ya nuna cewa hadari ne, amma rundunar sojin tace zata gudanar da bincike. Babban hafsan sojin kasar, Janar Hulusi Akar yayi tattaki da kansa zuwa yankin da lamarin ya faru don gane ma idanunsa.

Hakazlaika shima mataimakin Firai ministan kasar, Mehmet Simsek, da ministan tsaro Fikri Isik da ministan cikin gida Suleyman Soylu duk sun ziyarci inda lamarin ya auku, sa’annan tuni an sanar da shugaban kasar, Tayyip Erdogan.

Ko a watan Maris data gabata, wasu mutane bakwai ciki har da yan kasar Rasha mutum 4 suka mutu sakamakon hatsarin jirgin sama a babban birnin kasar, Instanbul bayan yaci karo da wayar Talabijin.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli nasarorin da Buhari ya samu

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani
NAIJ.com
Mailfire view pixel