Gwamnatin Buhari na daf da fara koyar da darussan lissafi da kimiyya a cikin harsunan uwa

Gwamnatin Buhari na daf da fara koyar da darussan lissafi da kimiyya a cikin harsunan uwa

Nan ba da dadewa ba, za a fara amfani da sabon tsarin koyar da darussan lissafi da kimiyya a makarantun firamare da sakandire dake fadin kasar nan, domin kara karfafa gwiwar dalibai wajen nazarin wadannan darussan yadda ya kamata da nufin farfado da fasahar kimiyya da kere kere a Nijeriya.

Ministan ma'aikatar kula da harkokin kimiyya da fasaha Ogbonnaya Onu shi ya bayyana haka a yayin kaddamar da wani kwamitin hadin gwiwa tsakanin ma'aikatar sa da kuma ma'aikatar ilimi, a wani bangare na kokarin ganin an bullo da sabbin dabaru na saukaka harkar samar da ilimi da kara zaburar da dalibai kan neman ilimin lissafi da kimiyya.

NAIJ.com ta samu labarin cewa ya ce, abin takaici ne yadda dalibai da sauran almajiran ilimi a kasar nan ke gudun darussan da suka shafi lissafi da kimiyya, wadanda kuma da su ne ake samar da fasahohin kirkira da bunkasa cigaban kasa.

Gwamnatin Buhari na daf da fara koyar da darussan lissafi da kimiyya a cikin harsunan uwa

Gwamnatin Buhari na daf da fara koyar da darussan lissafi da kimiyya a cikin harsunan uwa

Ya bayar da misali da kasashen Indiya da China wadanda ya ce, sun samu cigaba a harkar kirkira ne sanadiyyar bai wa darussan lissafi da kimiyya muhimmanci, wadanda kuma ake koyar da su cikin harsunan gida na gado ba da turanci ba.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel