Ba’a gayyaci Mikel da Moses ba a fafatwar da Najeriya zata yi da Afirka ta Kudu

Ba’a gayyaci Mikel da Moses ba a fafatwar da Najeriya zata yi da Afirka ta Kudu

- Kocin kungiyar kwallon kafa ta kasa, Super Eagles, Gernot Rohr ya sanar da jerin yan wasan da zasu buga da kasar Afirka ta kudu

- Kocin bai gayyaci Mikel Obi da Moses ba

Kocin kungiyar kwallon kafa ta kasa, Super Eagles, Gernot Rohr ya sanar da jerin yan wasan Super Eagles da zasu fafata a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin Nahiyar Afirka da Najeriya zata yi da kasar Afirka ta kudu a ranar 10 ga watan Yuni.

Fitattun yan wasan Najeriya, Mikel da Moses ba zasu samu daman buga wasan da za’a fafata a tsakanin kasashen biyu zai gudana ne a Najeriya, jihar Akwa Ibom ba.

KU KARANTA: Sabo da kaza: Damisa ta kashe mai kula da namun daji

NAIJ.com ta ruwaito dukkanin yan wasan biyu ne suka jefa kwallaye a ragar Algeria don tabbatar da Najeriya ta samun shiga gasar cin kofin Duniya.

Ba’a gayyaci Mikel da Moses ba a fafatwar da Najeriya zata yi da Afirka ta Kudu

Super Eagles

A ranar 29 ga watan Mayu ne Victor Moses ya angwance da tsohuwar budurwarsa uwar yayansa guda 2, don haka ne ba zai samu shiga wasan ba, yayin da shi kuma Mike ya samu rauni a kasar Sin.

Ba’a gayyaci Mikel da Moses ba a fafatwar da Najeriya zata yi da Afirka ta Kudu

Yan wasan Super Eagles

Yan wasan da aka sanar sun hada da:

Yan tsaron raga: Daniel Akpeyi, Ikechukwu Ezenwa, Dele Alampasu

Yan tsaron gida: Elderson Echiejile, William Ekong, Chigozie Awaziem, Tyronne Ebuehi, Kenneth Omeruo, Maroof Youssef, Abdullahi Shehu.

Yan wasan tsakiya: Ogenyi Onazi, Wilfred Ndidi, Mikel Agu, John Ogu, Oghenakaro Etebo, Alhassan Ibrahim.

Yan wasan gaba: Ahmed Musa, Kelechi Iheanacho, Olarewaju Kayode, Henry Onyekuru, Alex Iwobi, Victor Osimhen, Simon Moses.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Nasarorin Buhari a shekaru 2

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Majalisar dattawa ta bukaci rundunar sojin Najeriya da ta dawo da jami’in da aka kora bisa kuskure

Majalisar dattawa ta bukaci rundunar sojin Najeriya da ta dawo da jami’in da aka kora bisa kuskure

Majalisar dattawa ta bukaci rundunar sojin Najeriya da ta dawo da jami’in da aka kora bisa kuskure
NAIJ.com
Mailfire view pixel