Takara 2019: Matasan jihar Kano sun yi kira da babban murya ga Kawu Sumaila

Takara 2019: Matasan jihar Kano sun yi kira da babban murya ga Kawu Sumaila

- Wata kungiyar matasa tayi kira ga Kawu Sumaila daya amsa kiran su a shekarar 2019

- Sun ce Kawu Sumaila ya dace ya wakilici yankin a majalisar dattawa

Wata kungiyar matasan jihar Kano mai zaman kanta mai taken ‘Kano South Concerned Citizens and Development (KSCCD)’, wato matasan kudancin Kano masu karajin cigaban yankin sun yi kira ga Kawu Sumaila daya amsa kiran su a shekarar 2019.

Matasan sun bayyana mashawarcin shugaban kasa a fannin majalisar wakilai, Alhaji Kawu Sumaila a matsayin mutumin daya dace ya wakilici yankin a majalisar dattawa a shekarar 2019, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA: Najeriya zata fitar da doya ƙasashen Turai Najeriya zata fitar da doya ƙasashen Turai

Cikin wata sanarwa da majiyar NAIJ.com ta samu ta bakin shugaba da sakataren kungiyar, kwamared Habibu Sani Aliyu da Kwamared Nura Shehu Gaya suka fitar, sun ce kwarewar Kawu Sumaila a aiki yasa suka ga cancantar ya wakilci yankin a majalisar dattijai a zabukan 2019.

Takara 2019: Matasan jihar Kano sun yi kira da babban murya ga Kawu Sumaila

Kawu Sumaila

A cewarsu, muddin aka zabi Kawu, toh zai tabbatar da yayi dukkan mai yiwuwa wajen ganin sun taimaka ma manufofin shugaban kasa Muhammadu Buhari musamman wajen ciyar da kasa gaba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Muna bukatar sabbin shuwagabanni:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel