Manyamanyan alkawura 5 da Buhari ya dauka ya kuma kasa cikawa

Manyamanyan alkawura 5 da Buhari ya dauka ya kuma kasa cikawa

A wani shiri da gwamnatin tarayya wadda Shugaba Buhari ke jagoranta ta kaddamar a ranar litinin din da ta gabata. Mai magana da yawun gwamnatin kuma ministan yada labaran ta Alhaji Lai Muhammad ya bayyana da babbar murya cewa su fa sun cika dukkan alkawuran da suka daukar wa al'ummar kasar nan.

Ministan ya kuma kara da cewa shirin nan na rage radadin talauci a kasar ya samu gagarumar nasara ba ko yar kadan ma a cikin shekaru 2 kacal da fara shi.

NAIJ.com tayi wani dan bincike inda ta gano wasu alkawurra 5 manya da shugaba Buhari da jam'iyyar sa ta APC suka daukar wa jama'a a lokacin yakin neman zabe amma kuma suka kasa cikawa.

Gasu kamar haka:

1. Bada tallafin alawus alawus na kudi ga matasan da suka gama yi wa kasa hidima amma kuma basu samu aiki ba don su ja jari su fara sana'a.

2. Samar da aiyyukan yi har guda 720,000 ga matasa a dukkanin jihohin kasar nan 36 inda kowace jiha za'a samar mata aikin yi 20,000.

Manyamanyan alkawura 5 da Buhari ya dauka ya kuma kasa cikawa

Manyamanyan alkawura 5 da Buhari ya dauka ya kuma kasa cikawa

3. Kawar da banbance banbance a wajen aikin yi ta hanyar goge tabbacin zama dan jiha kafin mutum ya iya samun aiki.

4. Hana dukkanin jami'an gwamnati da masu rike da mukaman siyasa zuwa kasashen waje neman magani inda yanzu haka shi kansa shugaban Buhari yana kasar Ingila neman maganin.

5. Samar da ingantacciyar wutar lantarki da takai yawan mega wat 20,000 a cikin shekaru 4 inda yanzu haka aka kasa samar da mega wat 5,000 ma.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel