Atiku ne maganin matsalolin da Najeriya ke fuskanta a yanzu – Farfesa Olatunbosun

Atiku ne maganin matsalolin da Najeriya ke fuskanta a yanzu – Farfesa Olatunbosun

- Farfesa Dupe Olatubosun ya ce,tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku ya cancanci zama shugaban kasar Najeriya

- Olatunbosun ya ce shine zai iya warware matsalolin da kasar ke fuskanta a yanzu

- Farfesan yace taimako da Atiku ke yi da himmarsa na cigaban inganta bangaren Ilimi yasa ya fita daban daga cikin wasu shuwagabannin

Wani masani a harkan tattalin arzikin noma, Farfesa Dupe Olatubosun ya bayyana cewa, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar kuma daya daga cikin manyan jiga-jigan Jam’iyyar APC ya cancanci shugabancin Najeriya.

Olatubosun dake malamin Jami’a kuma mai rike da masana’antu daban-daban ya yi la’akari da irin halin matsin da kasa ke ciki a yanzu tare da cewa shuwagabani irin su ne zasu iya saita kasa kuma shi ya cancanci shugabancin Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Idan ka ji abin da ‘Yan Najeriya su ka yi asara a tsarin MMM sai ka yi kukaIdan ka ji abin da ‘Yan Najeriya su ka yi asara a tsarin MMM sai ka yi kuka

Atiku ne maganin matsalolin da Najeriya ke fuskanta a yanzu – Farfesa Olatunbosun

Farfesa Olatunbosun ya ce Atiku ne maganin matsalolin da Najeriya ke fuskanta a yanzu

Ya ce kwarin guiwansa na sanin yadda ya kamata a tafiyar da harkokin kasa musamman a lokacin da Najeriya ke fama da matsaloli barkatai yasa ya bayyana haka.

Farfesan yace taimako da Atiku ke yi da himmarsa na cigaban inganta bangaren Ilimi yasa ya fita daban daga cikin wasu shuwagabannin, kuma yana daya daga cikin mutanen da kasa ke bukata a yanzu don saita yanayin yadda harkoki ke tafiya kuma shi zai iya raya cigaba tattalin arzikinta a matsayinsa na wanda ya taba mulkan Najeriya.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Zaben Anambara yana daga cikin mafi muni zabe da aka gudanar tun 1999 da Najeriya ta dawo mulkin dimokradiyya - Kungiyar PLAC

NAIJ.com
Mailfire view pixel