Dalilin da yasa Osinbajo bai rattaba hannu kan kasafin kudin 2017 ba – Fadar Shugaban kasa

Dalilin da yasa Osinbajo bai rattaba hannu kan kasafin kudin 2017 ba – Fadar Shugaban kasa

Fadar shugaban kasa tayi bayanin dalilin da yasa mukaddashin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, bai rattaba hannu kan takardan kasafin kudin 2017 ba har yanzu.

Tace har yanzu ana neman shawarwari ne game da rattaba hannu kan takardan.

Babban mai baiwa shugaban kasa shawara akan harkokin majalisar dattawa, Sanata Ita Enang, “ Bisa ga bukatan da mukayi kan abin da ke faruwa da takardan kasafin kudin 2017, ku sani cewa har yanzu ba’a shirya rattaba hannu ba saboda har yanzu ana neman shawarwari.”

Dalilin da yasa Osinbajo bai rattaba hannu kan kasafin kudin 2017 ba – Fadar Shugaban kasa

Dalilin da yasa Osinbajo bai rattaba hannu kan kasafin kudin 2017 ba – Fadar Shugaban kasa

A ranan 16 ga watan Mayu, 2017, majalisar dattawa tayi bayanin cewa bukatan shaihantar da kasafin kudin ne dalilin da akayi jinkiri wajen aika takardan ga bangaren zantarwa.

KU KARANTA: Buhari na hannun kwararru - Lai Mohammed

Yayinda yake magana da manema labarai akan jinkirin, shugaban kwamitin labarai da harkokin jama’a, Sanata Sab Abdullahi, yace wajibi ne kwamitin ta gama ayyukan da take yi sosai.

Babban lauya, Femi Falana ya bayyana cewa ba zai yiwu mukaddashin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya rattaba hannu kan kasafin kudin kasa ba.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Surukar marigayi Bilyaminu, Maimuna Aliyu tana kotu bisa tuhumar wawurar dukiyar gwamnati

Surukar marigayi Bilyaminu, Maimuna Aliyu tana kotu bisa tuhumar wawurar dukiyar gwamnati

Surukar marigayi Bilyaminu, Maimuna Aliyu tana kotu bisa tuhumar wawurar dukiyar gwamnati
NAIJ.com
Mailfire view pixel