Wani mutumi ya sace mahaifin sa, sannan ya karbi naira miliyan 1 a matsayin kudin fansa

Wani mutumi ya sace mahaifin sa, sannan ya karbi naira miliyan 1 a matsayin kudin fansa

- An kama wani mutumi da ya hada hannu da wasu mutane don su yi garkuwa da mahaifin sa

- Al’amarin ya afku ne a jihar Oyo

- Sun karbi naira miliyan daya a mastayin kudin fansa

An kama wani mutumi da ya hada hannu da wasu mutane don su yi garkuwa da mahaifin sa.

Kwamishinan yan sandan jihar Oyo, Abiodun Odude ya tisa keyar mai laifin tare da sauran mutanen a ranar Laraba, 31 ga watan Mayu.

Mr. Odude ya bayyana cewa an gabatar da garkuwa da mahaifin mai laifin ne a Igboora karamar hukumar Ibarapa Central a ranar 17 ga watan Mayu da misalin karfe 6 na yamma.

KU KARANTA KUMA: Boko Haram: Gaskiya da sanin aikin Buhari ya sa Sojojin Najeriya su ka kara damara

Wani mutumi ya sace mahaifin sa, sannan ya karbi naira miliyan 1 a matsayin kudin fansa

Wani mutumi ya sace mahaifin sa, sannan ya karbi naira miliyan 1 a matsayin kudin fansa

“Mai laifin ya ce ya kamu kaso da bai kai naira miliyan day aba daga kudin fansan da ya karba koda dai ya bayyana cewa maaifinsa bai taba yi masa laifi ba," inji shi.

Ya bayyana cewa za’a tura masu laifin kotu da zaran an kammala gudanar da bincike.

A wani al’amari makamancin wannan NAIJ.com ta samu labarin cewa an yi ram da mutane shidda da ake zargi da garkuwa da shugaban gidan man Bovas Oil and Gas Limited.

Abubuwan da aka gano daga masu laifin sun hada da makamai, motoci tara, babur daya, naira miliyan 1.2, kayan kide-kide, wuka da kuma wayoyi.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel