Kuma dai: Fadar Shugaban kasa tayi amai ta lashe a game da kasafin kudi

Kuma dai: Fadar Shugaban kasa tayi amai ta lashe a game da kasafin kudi

– Fadar Shugaban kasa tace ba a gama aiki game da kasafin kudi ba

– Osinbajo yace har yanzu yana cigaba da tuntubar ‘Yan Majalisu

– A yau dai an shiga Watan Yuni kuma har yanzu shiru

Jiya kun ji cewa Mukaddashin Shugaban kasa bai sa hannu a kan kasafin kudin bana ba

Har mun samu labari cewa za a rattaba hannu kan kundin kasafin Yau

Sai ga shi kuma mun ji har yanzu ba a shirya rattaba hannun ba

Kuma dai: Fadar Shugaban kasa tayi amai ta lashe a game da kasafin kudi

Ba a gama aiki game da kasafin kudi ba

Bayan mun samu rahoto cewa za a rattaba hannu kan kasafin kudin a Yau Alhamis 1 ga Watan Yuni, sai kuma mu ka ji cewa har yanzu Mukaddashin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo na tuntubar ‘Yan Majalisa ne game da kasafin kudin.

KU KARANTA: Wani tsohon Gwamna na harin kujerar Shugaban kasa

Kuma dai: Fadar Shugaban kasa tayi amai ta lashe a game da kasafin kudi

Yaushe za a rattaba hannu kan kasafin kudin bana?

Mai magana da bakin Farfesa Yemi Osinbajo ya tabbatar da cewa har yanzu dai ba a kammala aikin kasafin kudin ba. A baya dai da mun ji cewa Yemi Osinbajo ya gayyaci shugabannin Majalisa zuwa Aso Villa game da aikin kundin kasafin.

Kusan makonni biyu kenan da Majalisa ta kammala aikin kasafin kudin wannan shekarar bayan kusan wata shida ana fama. Sai dai har yanzu Mukaddashin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo bai rattaba hannu a kundin kasafin kudin ba.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wai kudin Najeriya zai kara daraja kuwa?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose
NAIJ.com
Mailfire view pixel