Najeriya zata fitar da doya ƙasashen Turai

Najeriya zata fitar da doya ƙasashen Turai

- Ministan harkokin noma Audu Ogbeh ya bayyana cewa za'a fara fitar da doya

- Nan bada dadewa ba sundukai masu dauke da tarin doya yar Najeriya zasu fara fita akan hanyarsu ta zuwa kasashen Turai

Ministan harkokin noma Audu Ogbeh ya bayyana cewa nan bada dadewa ba sundukai masu dauke da tarin doya yar Najeriya zasu fara fita akan hanyarsu ta zuwa kasashen Turai.

Minista Ogbeh yace bada tabbacin a ranar 29 ga watan Yunin bana ne za’a fara fitar da doyan, ya bayyana haka ne yayin ganawa da manema labaru a ranar litinin 29 ga watan Mayu, inda yake bayyana nasarorin da suka samu.

KU KARANTA: An kamo yar Fim ɗin Hausa a aka yanke ma hukuncin kisa, amma ta arce daga gidan yari (Hoto)

Ministan ya bayyana cewa fannin shanin noma zai dawo martabarsa a matsayin bangaren dake fitar da abinci da kayan noma zuwa kasashen waje. Ministan yace yanzu haka kasar na fitar da kayayyakin gona da wake zuwa Indiya.

Najeriya zata fitar da doya ƙasashen Turai

Audu Ogbeh

“A nan da shekaru biyu masu zuwa Najeriya zata cigaba da fitar da kayan noma kasashen waje, sa’annan a ranar 29 ga watan Yuni za’a fara aikawa dasu. Nan bada dadewa ba za’a cigaba da fitar da Cocoa zuwa kasar Vietnam. Lokaci ne kawa ake jira.

“Ya zama dole mu fara sarrafa abinda muke bukata. Abubuwa kalilan muke amfani dashi kamar su kayan marmari, shinkafa, siga, madara, gero da rogo. Sa’annan kaga farashin kaya ya tashi, amma saboda karyewar naira, shine dalilin daya sa haka.” Inji Minista.

A wani labarin kuma, NAIJ.com ta ruwaito shugaban jam’iyyar APC Cif Oyegun ya bada bahasin irin tabarar da gwamnatin jam’iyyarp PDP tayi ma wannan kasar a shekarar 16 da tayi, daga nan yace ya zama dole yan Najeriya su yaba ma shugaba Buhari saboda tafiyar da kasar yadda ya kamata.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Shuwagabannin Najeriyda da sake

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel