Gwamnatin Saudiyya ta kai samame kan masu jabun ruwan Zam-Zam

Gwamnatin Saudiyya ta kai samame kan masu jabun ruwan Zam-Zam

- Rahotanni daga kasar Saudiyya sun bayyana cewa hukumar kula da ingancin abinci ta kasar ta ce ta halaka dubban kwalaben ruwan zamzam na jabu

- Sannan kuma hukumar ta rufe gidaje da dama da ake yin ruwan a wani farmaki da ta kai a fadin kasar

- Hukumar ta gargaɗi mutane da su kula domin kada su fada tarkon masu samar da jabun ruwan na zamzam

Rahotanni daga kasar Saudiyya sun bayyana cewa hukumar kula da ingancin abinci ta kasar ta ce ta halaka dubban kwalaben ruwan zamzam na jabu sannan kuma ta rufe gidaje dake da alaka da samar da ruwan a wani farmaki da ta kai a ilahirin kasar.

Wannan rahoton ya bayyana ne a Jaridar Saudiyya mai suna Saudi Gazette inda tace mutane na yin ruwan jabu na zam-zam ne saboda tsananin bukatar zamzam da al'umma ke da ita musammam don yin buda-baki a wata mai alfarma ta Ramadan.

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari na hannun kwararru - Inji Ministan yada labarai

Gwamnatin Saudiyya ta kai samame kan masu jabun ruwan Zam-Zam

Gwamnatin Saudiyya ta kai samame kan masu jabun ruwan Zam-Zam

Hukumar ta gargadi jama’a da su kula kada su fada tarkon masu yin jabun ruwan zamzam, lamarin da ya haifar da damuwa ga hukumomin kasar ta Saudi Arabia inda mahajjata daga kasashen daban-daban kan sayi ruwan zamzam din da dama su kai gida.

Don tabbatar da samun ingantaccen ruwan zamzam, gwamnati ta yi wa wasu zababbun kantuna rajistar sayar da ruwan.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel