Gwamna Bello ya nada sabin sakatarori 17, ya kuma yi ritaya wasu 16

Gwamna Bello ya nada sabin sakatarori 17, ya kuma yi ritaya wasu 16

- Gwamnan jihar Neja nada sabin sakatarori na dindin yayin da kuma ya yi ritaya wasu 16

- Gwamnati zata yi karin ma'aikatu 3 da kuma daukan ma’aikata masu digiri 250

- Sakatarori 8 za su ci gaba da aikin su yayin da wasu 2 kuma wadanda aka ba rikon kwariya za a tabbatar da su

Gwamna Abubakar Bello na jihar Nijar a ranar Talata, 30 ga watan Mayu ya yi ritaya wasu sakatarori 16 inda kuma ya nada sababbi 17.

Babban mataimakin na musamma kan harkokin watsa labarai na gwamnan jihar, Mista Jide Orintunsin, ya bayyana cewa gwamnan ya umarci sakatarori da su ci gaba da hutun ritaya a nan da nan.

NAIJ.com ta ruwaito cewa, Orintunsin ya ce sakatarori 8 za su ci gaba da aikin su yayin da wasu 2 kuma wadanda aka ba rikon kwariya za a tabbatar da su.

Gwamna Bello ya nada sabin sakatarori 17, ya kuma yi ritaya wasu 16

Gwamnan jihar Neja Abubakar Bello

"Karin ma'aikatu 3 da kuma daukan ma’aikata masu digiri 250 na daya daga cikin kokarin cin gajiyar ma'aikataun da kuma bunkasa ta.

KU KARANTA: Fadar shugaban ƙasa tayi watsa watsa da gwamna Fayose, Karanta

Sababbin ma'aikatun sun hada da; Ma'aikatar gandun daji da kuma dabbobi, ma'aikatar ma'adanai da ma'aikatar al'adu da yawon shakatawa, kawo yawan ma'aikatun a jihar zuwa 18 daga 15.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon inda mai martaba sarki Sanusi ya shawarci shugabannin Najeriya da shugabanci na nagari

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani
NAIJ.com
Mailfire view pixel