Buhari ba zai iya kakkabe cin hanci a cikin shekaru 4 ba – Inji wani tsohon gwamna

Buhari ba zai iya kakkabe cin hanci a cikin shekaru 4 ba – Inji wani tsohon gwamna

- Cif Bisi Akande ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai iya yaki cin hanci da rashawa a shekaru 4 ba

- Akande ya ce yaki da cin hanci da rashawa wani abu ne mai wuya

- Akande ya sake cewa sojoji ne suka kawo cin hanci da rashawa kasancewar su a mulki na shekaru 39

Tsohon gwamnan Jihar Osun Cif Bisi Akande, ya yi Allah wadai da karuwan cin hanci da rashawa a kasar, inda ya jajirce cewa yaki da cin hanci da rashawa wani abu ne mai wuya wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai iya shawo kai ba a cikin shekaru hudu kacal da mulki.

NAIJ.com ta ruwaito cewa, tsohon gwamnan ya bayyana haka ne a cikin wata hiran da ya yi da jaridar SUN.

A cikin kalmominsa: "Cin hanci da rashawa a Najeriya ya zama ruwan dare saboda mulkin soja ta gabatar da ita. Lokacin da sojoji suka karbi mulkin kasar sun kasance shekaru 39 a karagar mulki, cin hanci da rashawa ne kawai abin da suka bar muna. Saboda haka, kawo karshen cin hanci da rashawa, dole ne muyi hankuri kuma dole ne mu hada hannu a matsayin mu na ‘yan Najeriya domin kawo karshen al’amarin.”

Buhari ba zai iya kakkabe cin hanci a cikin shekaru 4 ba – Inji wani tsohon gwamna

Shugaban kasa Muhammadu Buhari na gaisawa da gwamnan jihar Ogun Ibikunle Amosun

“Alal misali, akwai mutanen da suke ganin cewa dole ne zai sun bada cin hanci kafin su ko kuma kafin 'ya'yansu su ci jarrabawa. Zai lokacin da muka iya kaucewa irin wannan tunanin cin hanci da rashawa daga gidanjenmu, ba za mu iya cimma wata nasara ba.”

KU KARANTA: Fadar shugaban ƙasa tayi watsa watsa da gwamna Fayose, Karanta

Buhari ne kawai shugaban wanda zai iya warware masalolin da Najeriya ke fuskanta a halin yanzu. Wannan shi ne dalilin da yasa ya kamata mu yi masa addu’a domin ya samu lafiya. Babu wanda zai iya ci galaba gaba daya kan yaki da cin hanci da rashawa.

Akande ya ce: “Cin hanci da rashawa na kisa.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ra'ayoyin 'yan Najeriya kan komawar shugaba Buhari Landan don duba lafiyarsa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose
NAIJ.com
Mailfire view pixel