Shugaba Buhari na hannun kwararru, inji Ministan yada labarai

Shugaba Buhari na hannun kwararru, inji Ministan yada labarai

- Ministan yada labarai Lai Muhammed yace Buhari na hannun kwararru

- Matar shugaba Buhari ta tafi dubo shi a asibiti

- An sami rade-radi tun bayan tafiyarsa asibiti 7 ga Mayu

A bayan kammala taron majalisar zababbu ta ministoci a fadar gwamnati dake Aso Rock Villa, ministan yada labarai yace shugaba Buhari yana hannun kwararru, don haka kada jama'a su razana ko su damu.

Ya furta hakan ne bayan da manema labarai suka tambaye shi ko akwai wani bayani daga bakin iyalin shugaban, bayan ziyarar da Matar sa Aisha Buhari ta kai ingilar domin gane wa idonta, jikin mijin nata.

KU KARANTA KUMA: 'Ina so in zama shugaban kasa' - Tsohon gwamna Donald Duke

Shugaba Buhari na hannun kwararru, inji Ministan yada labarai

Shugaba Buhari na hannun kwararru, inji Ministan yada labarai

NAIJ.com ta tuna cewa tun ranar 7 ga wata shugaba Buhari ya tafi jinya, kuma ba'a kara jin duriyarsa ba, kafin nan ma dai, baya iya fitowa aiki a fadar mulki. Ya kuma yi wata biyu a asibiti tun farkon shekarar nan.

Sannan kuma a jiya Talata, 30 ga watan Mayu ne uwargidan shugaban kasar, Aisha Buhari ta tafi kasar Ingila domin kai wa mijin nata ziyara a inda yake jinya.

Shekaru biyu kenan da shugaban yake mulki a Najeriya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Nasarorin shugaba Buhari a shekaru biyu da ya yi yana mulki

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel